Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (5)

Saboda karfin imanin Salmanul Farisi (RA) da shaukinsa na neman shiriya, ya sa Annabi (SAW) ya ba da shaida kan gaskiyar imaninsa. Buhari da Muslim sun ruwaito cewa” “Lallai Abu Huraira (RA) ya ce: “Mun kasance a zaune a wurin Annabi (SAW), sai aka saukar masa da Suratul Jumu’ati cewa: “Da wadansu mutane daga gare […]

Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (5)
Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (5)

Saboda karfin imanin Salmanul Farisi (RA) da shaukinsa na neman shiriya, ya sa Annabi (SAW) ya ba da shaida kan gaskiyar imaninsa. Buhari da Muslim sun ruwaito cewa” “Lallai Abu Huraira (RA) ya ce: “Mun kasance a zaune a wurin Annabi (SAW), sai aka saukar masa da Suratul Jumu’ati cewa: “Da wadansu mutane daga gare su, ba su i da riskuwa da su ba.” Sai na ce: “Suna daga su wane ne ya Manzon Allah?” Bai waiwaye shi ba, har ya tambaya sau uku. Ya ce “A cikinmu akwai Salmanul Farisi, sai ya dora hannunsa a kan Salmanu, sannan ya ce: “Da imani zai kasance a cikin (tauraruwar) Surayya, wasu mazaje ko wani namiji daga cikin wadannan zai dawo da shi (duniyar nan).”
Ka yi gaskiya ya Manzon Allah, mazaje daga mutanen da Salmanu ya fito daga cikinsu sun ba da gagarumar gudunmawa ga addinin Musulunci a lokacin da addinin yake bukatar haka domin tsare shi daga dasisar da makiya addinin suka yi yunkurin sanyawa cikinsa, musamman ta wajen tantance Hadisan karya da aka rika kokarin sanyawa a cikin addinin domin biyan bukatar masu son wargaza shi. Cikin irin wadannan jarumawa akwai Imam Muhammad bin Isma’il da aka fi sani da Buhari da Imam Muslim Alkushairiyyu da aka fi sani da Muslim da Tirmizi da Nisa’i wadanda suka yi ta kokarin tsabtace Hadisai, kuma dukkansu sun fito ne daga tsohuwar Daular Farisa inda Salmanu ya fito. Sannan akwai malaman Tafsiri da na Fikhu da na fannonin ilimi daban-daban da suka fito daga wannan yanki wadanda har duniya ta nade za a ci gaba da cin gajiyar ilimi da shiriyar da suka dora mutane a kai a daidai lokacin da duniyar Musulmi ta fadada ta hadu da majusawa da Alhlul Kitab da zindikai da mulhidai da suka yi kokarin rikita koyarwar Musulunci ko suka rika kalubalantar wasu koyarwarsa.
Hakika juriya da dauriya da gwagwarmayar da Salmanul Farisi ya yi wajen neman shiriya a daidai lokacin da duniya ta fada cikin duhun jahilci da tabewa ba karamin abin misali ne ga duk mai son shiriya ba. Galibin abin da ke kawao mana illa da koma baya muna tozarta koyarwar addini, muna jahiltarsa da kauce wa gwadabensa da kawar da kai daga gare shi a wannan zamani na faruwa ne saboda uzirori na kasala da gafala. Wani lokaci kuma saboda bin al’ada da haka na iske a tsakanin al’umma ko haka ake yi a garinmu ko unguwarmu ko gidanmu ko abokanmu ko tsoron shiga fitina da jarrabawa.
Ya kamata mu ci gajiyar samartakarmu da rayuwarmu don yin koyi da Salmanul Farisi wajen neman ilimi da shiriya, ya taso a cikin batacciyar al’umma, ya taso a cikin tsananin fitina da raunin iyali da gidan fasadi, amma ya mayar da kansa bako ya rabu da kayayyakin sha’awa da jin dadi ya shiga cikin tsananin fitina a kokarinsa na neman shiriya.
Duk wanda ya bari sha’awarsa da shubha suka samu galaba a kansa ba zai ribaci rayuwarsa ba, ba zai ladabtar da kansa ba, maimakon haka sai ya rika dora laifin gazawarsa kan al’ummar da ya taso ko iyalinsa ko kasarsa. Kamar yadda muke ciki a yanzu a kasar nan, mutane ba su wani yunkuri na komawa ga Allah da kiyaye abubuwan da za su kai su ga halaka, sai su rika cewa kasa ta lalace, duk wanda ya tsaya kan zai yi gaskiya zai tashi a tutar babu, da haka suke halatta wa kanwunansu abubuwan da suke haram kamar cin hanci da rashawa da almundahana da danne dukiyar masu rauni da sauran munanan abubuwa.
Ina ruwanka da lalacewar mafi yawan al’umma? Kai da za a yi maka shari’a kai kadanka kan abin da kai aikata me ya hada ka da cewa tunda al’umma ta lalace bari kai ma ka lalace? Wa ya gaya maka a gobe kiyama Allah zai yi maka hisabi ne a matsayinka na dan Najeriya ko dan wata jiha a Najeriya? Babu ruwan Allah da wadannan rabe-raben kasashe ko jihohi,duniya gaba daya a wurin Allah dunkule take, duk inda ya ajiye ka abin da yake so ka yi masa da’a ka yi wa ManzonSa (SAW) da’a. Idan har kana jin al’umma ko unguwa ko gari ko jiha ko kasar da kake zaune ba za su ba ka damar yin biyayya ga Allah ba, me zai hana ka koma wata unguwa ko jiha ko kasa inda kake ganin za ka samu damar yi wa Allah da’a domin ka tsira gobe kiyama?
Wajibi ne mu kwaikwayi himmar Salmanul Farisi, mu koyi sadaukarwarsa da himmarsa, mu dubi yadda ya rabu da gatar da yake da ita a wurin mahaifinsa, mu dubi yadda ya rabu da jin dadin dukiyar mahaifinsa ya rabu da iyayensa saboda suna cikin bata, ya yi ta tafiya daga wannan gari zuwa wancan gari daga wannan kasa zuwa wancan kasa, ya fada a wancan kwazazzabo, ya shiga wannan hamada ga zafin rana ga dukan ruwa dukj a kokarinsa na neman shiriya domin ya hadu da Allah lami lafiya gobe kiyama.
Salmanu ya yi wannan tafiye-tafiye ne saboda shaukinsa na haduwa da Allah har sai da ya koma ga Allah yana kan mafi alherin addini a bayan kasa wato Musulunci. Ya koma ga Allah yana mai gudun duniya mai kwadayi zuwa ga Lahira, ya koma ga Allah yana mai ibada, malami, mai jihadi a tafarkin Allah!
Haka ake son kowane Musulmi ya kasance, ya yi amfani da kudirarsa da iradarsa wajen mayar da abin da yake mai wahala ya zama mai sauki ta wajen kokarinsa na neman gaskiya da gano shiriya. Allah Ka kara yarda da Salmanul Farisi wanda ya bar mana abin misali wajen neman shiriya da gaskiya.
A yayin da muke kammala wannan darasi kan gwagwarmayar Salmanul Farisi, tambayyarmu ita ce: Shin akwai mai son koyi da shi? Allah Yana nan a inda bawanSa yake zatonsa, kamar yadda ya tabbata a cikin wani Hadisin kudisi.