Salomon Lar ya rasu
Gwamnatin Jihar Filato ta bayyana cewa tsohon Gwamnan faran hula na fako a jihar Cif Solomon Daushep Lar ya rasu. Cif Solomon Lar ya rasu ne a wani asibiti a kasar Amurka bayan doguwar jinya.Gwamnan Jihar Mista Jonah Dabid Jang ne ya shaida wa manema labarai haka a Jos a shekaranjiya Laraba, inda ya ce, […]

Gwamnatin Jihar Filato ta bayyana cewa tsohon Gwamnan faran hula na fako a jihar Cif Solomon Daushep Lar ya rasu. Cif Solomon Lar ya rasu ne a wani asibiti a kasar Amurka bayan doguwar jinya.
Gwamnan Jihar Mista Jonah Dabid Jang ne ya shaida wa manema labarai haka a Jos a shekaranjiya Laraba, inda ya ce, “Ya rasu ne da misalin karfe 3:00 na dare agogon Amurka, (daidai da karfe 9:00 na rana agogon Najeriya).
An haifi Cif Lar ne a kauyen Pongaa da ke karamar Hukumar Langtang da ke Jihar Filato a watan Afrilun 1933. Mahaifinsa manomi ne yayin da mahaifiyarsa mai ginin tukwane. Ya halarci makarantar firamare ta Sudan United Mission Primary School da ke Langtang, sannan ya wuce Kwalejin Horon Malamai ta Gindiri inda ya samu takardar koyarwar a firamare. Bayan shekara biyu ya sake komawa Gindiri don kwas din horon manyan malamai inda ya samu babbar takardar koyarwar.
An zabi Lar a matsayin kansila a En’e ta Langtang a Janairun 1959. Sannan aka zabe shi dan majalisar tarayya a ranar 12 ga Disamban 1959 a karkashin Jam’iyyar United Middle Belt Congress (UMBC). An sake zabensa a 1964, ya taba zama sakataren majalisa ga Firayi Ministan Najeriya Sa Abubakar Tafawa balewa kuma karamin Minista a Ma’aikatar daukar Ma’aikata ta Tarayya.
Bayan kawar da gwamnatin farar hula Solomon Lar ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello inda ya kammala digirinsa a fannin shari’a a 1970, sannan ya zama cikakken lauya a 1971. Dagan an ne ya fara aikin lauya a matsayin mai zaman kansa, kuma ya zama abokin tagwaicin kafa kungiyar ba da tallafin lauyoyi ta Najeriya kuma sakarenta na farko.
Ya rike mukamai da dama a kungiyoyi da hukumomi kafin ya zama wakili a kwamitin tsarin mulki a 1977-1978. Kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin Mai shari’a Ayo Irikefe wanda ya ba da shawarar kara jihohin kasar nan zuwa 19 daga 12 a lokacin mulkin Murtala da Obasanjo.
Ya yi Ministan Harkokin ‘’Yan sanda a zamanin mulkin Janar Sani Abacha, sannan a yayin yunkurin dawo da mulki hannun farar hula a 1998, ya zama shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa na farko,
Aiki na karshe day a yi wa kasar nan shi ne wanda a watan Fabrairun shekarar 2010 Shugaba Goodluck Jonathan ya nada shi Shugaban Kwamitin Shugaban kasa da aka dora wa alhakin samo hanyoyin da za hana sake tashin hankali a garin Jos fadar Jihar Filato.