Salon takun gwamnatin Buhari ya dada jawo matsalar tattalin arziki – Yusha’u Aliyu]
Malam Yusha’u Aliyu masanin tattalin arziki ne da yake sharhi a kan tattalin arzikin kasa a kafofin watsa labarai na gida da waje. Aminiya ta zanta da shi inda ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza game da manufofinta na rufe kan iyakar kasar nan domin bunkasa noma da kuma kwan-gaba-kwan-baya a tsarin Babban Bankin […]

Malam Yusha’u Aliyu masanin tattalin arziki ne da yake sharhi a kan tattalin arzikin kasa a kafofin watsa labarai na gida da waje. Aminiya ta zanta da shi inda ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza game da manufofinta na rufe kan iyakar kasar nan domin bunkasa noma da kuma kwan-gaba-kwan-baya a tsarin Babban Bankin Najeriya kan musayar kudaden kasar waje da sauransu:
Aminiya: A yanzu jama’a na koke-koken kan matsin tattalin arziki a ganinka mene ne tushen matsalar?
Matsala ce mai tarihi sai kuma abin da tattalin arzikin ya tarar. Tun a shekarar 2014 Ministar Kudi ta lokacin Dokta Ngozi Iweala ta yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar nan zai fuskanci matsalar durkushewa. Ta jagoranci gabatar da wasu tsare-tsare wadanda take ganin idan aka bi za a iya kauce wa hakan. Sai dai ko a lokacin da ta gabatar da tsarin, tattalin arzikin ya fara samun nakasu saboda wasu dalilai. Na farko harkoki sun yi sanyi sakamakon rashin tsaro, na biyu ba masu shigowa daga waje su zuba jari a cikin kasar nan shi ma saboda rashin tsaro, na uku ’yan siyasar kasar sun rabu kashi biyu, babu tabbacin wane bangare ne zai samu nasara a tsakanin masu mulki da masu ra’ayin canji. Wannan ya jawo gagarumin tsaiko, sai kuma wani babban abu da ya shafi tattalin arzikin duniya gaba daya wato faduwar darajar man fetur wanda siyasar duniya a kan man fetur ta haddasa. Kuma akwai yanayin takun wannan gwamnatin ita kanta, na rashin hanzari wajen aiwatar da abubuwa inda ta shafe kusan shekara guda ba a san inda ta dosa ba. Duk da wadannan tarin matsaloli kasuwar hada-hadar hannun jari na Najeriya ta tashi sama da kashi 53 cikin 100 a lokacin da wannan gwamnatin ta karbi mulki saboda yarda da ake da ita ga Shugaba Buhari, al’amarin da ba a taba ganin irin haka ba. Amma saboda jinkirin aiwatar da abubuwa irin na gwamnatin sai hannun jari ya sake rugujewa.
Wadanne shawarwari tsohuwar Ministar ta bayar da kake jin ba a aiwatar da su ba?
Na farko ta ba da shawarar a rage kashen kudi a kan abubuwa marasa tasiri, amma kowa ya san irin facakar da aka yi da kudi a lokacin yakin neman zaben 2015, da jam’iyya mai mulki (PDP) ta yi, sai dai ma iya cewa a wannan gwamnatin ana aiwatar da wannan tsari. Na biyu Ministar ta ba da jerin abubuwan da ta bukaci a hana shigo da su daga waje domin bunkasa wanda ake samarwa a nan gida tare da kara wa kudinmu na ajiya da ke waje karfi. To wannan har yanzu bai samu cikakken aiwatarwa ba saboda har yanzu ana shigo da wasu daga cikin abubuwan da aka hana. Baya ga wadannan matsaloli, Babban Bankin Najeriya ya yi ta kawo dokoki masu tufka-da-warwara a bangaren hada-hadar canjin kuddaden waje. Kuma sakamakon rashin tattara cikakken adadin hada-hadar kudi da kasar nan ke bukata a bangaren, domin sanin adadin kudin canji da za a bukata, to gibin da ake samu na sa Naira tana kara faduwa.
Aminiya: Sai dai gwamnati ta danganta rashin bayar da Dala a kan karancinsa a hannunta da faduwar farashin mai ya haifar, me za ka ce?
Eh akwai wannan, amma dai muna bayanin musabbabi ne, ka ga dole a ambato wannan. Kuma ina Dala wajen biliyan 20 da Sarkin Kano Sanusi ya ce sun yi layar zana wanda daga baya bayan wannan gwamnatin ta gano inda aka karkatar da su, a yi amfani da kudin mana. Kuma tun farko ta hannun Babban Bankin ne kudin suka sulale zuwa bankunan kasuwanci, zuwa ’yan canji, sannan hannun wadanda suka amfana da su.
Ka yi misali da Sarki Sanusi, ga shi ya soki tsarin bai wa wadansu canji kudi bisa rahusa a kwanan nan, inda ya ce yin hakan arzuta wadansu tsiraru ne da talauta kasa?
To, bayan daina bai wa ’yan canji kudin gwamnati ta kuma bi bankuna ta yi musu ta tarnaki a kan yadda suke gudanar da hada-hadarsu na kudin waje, inda ta gitta wasu tsaurararan matakai a tsarinsu na safarar kudi ta banki da ake kira Money Transfer, wanda ’yan kasuwanmu da masu karatu a waje da masu zuwa jinya da sauransu ke amfani da shi. Haka ’yan Najeriya da ke aiki da wasu cibiyoyi na kasashen waje a nan kasar su ma ba su tsira ba, saboda ba dama su karbi kudinsu na albashi ta bankunan Najeriya sai sun je waje kamar kasar Nijar inda bankunansu ke ba su kudin a Naira a maimakon Dala. Hakan na bai wa bankunan na Nijar damar amfana da kudin waje su kuma bankunanmu su rasa. Wadannan abubuwan sun jawo karin karancin Dala.
Me za ka ce a kan tsarin asusun bai-daya da gwamnatin ta kawo da ake korafin yana jawo tsaiko wajen gudanar da abubuwa a ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati da makarantu?
Tsarin asusun ajiya na bai-daya yana da kyau! Kamar kai ne kake da kamfanonin da ke da asusu mabambanta inda kowane kamfani ke abin da ya ga dama, to mene ne laifi idan ka ba da umarnin kowane kamafani ya ajiye maka kudinka a asusu guda. Wannan tsari ne da zai bai wa gwamnati damar sanin inda kudinta yake da adadinsa da halin da yake ciki.
Mece ce shawararka ga gwamnati kan za a samu saurin fita daga kangin tawayar tattalin arzikin kasa?
Shi dai mulki ana yi a samu nasararsa ne da tausayi a dukkan wasu manufofi da za a kirkiro. Shi ko tausayi na farawa ne daga samar da walwala, walwala na samuwa ne idan akwai zirga-zirgar kudi da samun abinci da sufuri cikin sauki. To hanyar da gwamnati za ta bi ta saukake rayuwa ta hada da rage kudin ruwa da bankunan kasuwanci ke dora wa masu neman zuba jari ko masu neman bunkasa harkokinsu. karin kudin ruwa da bankunan suka yi daga kashi 12 cikin 100 zuwa 14 a cikin 100 ya yi yawa.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i da abin ya fusata shi cewa ya yi wannan kudin ruwan sai masu hada-hadar kwayoyi ne kadai za su iya biya ba masu masana’antu ba. Na biyu wannan rufe kan iyaka da aka yi da sunan taimaka wa manoma ba alheri ba ne, babban abin da ya kamata kasa mai girman kasa da yawan jama’a kamar Najeriya ta yi, shi ne ta ci gajiyar hada-hadar da ake yi ta duk kan iyakokinta ta hanyar yin karin kudin haraji, wannan kadai zai samar mata da karin kudin shiga. Idan karancin ma’aikatan Kwastam ne ake da shi sai a dauki karin ma’aikata a Kwastam, ga dimbin jama’a suna neman aiki. Yawancin al’ummar da ke jihohi kan iyaka sun dogara ne da sana’ar fito musamman a nan bangaren Arewa wanda al’ummarta ne suka fi cutuwa a yanzu saboda girman yankinsu da ke iyaka da kasashe makwabta.
Da shi suke rike ’ya’yansu da ke makaranta su rike iyayensu, amma duk yanzu an hana su hada-hadar nan da an ga mutum ya shigo da kayan abinci sai a harbe shi. Yaya za a ce kasa kamar Najeriya sai ta yankin ruwa kadai za a shigo da abinci. Rufe kan iyaka da kuma bunkasa noma abubuwa biyu ne mabambanta da bai kamata a hada su ba, kowa ya san abin da zai kashe lagon shigo da abu shi ne haraji, shi ko bunkasa noma shi ne samar da taki da makamantansu ga manoma. Ai tumatur da ake nomawa har ana zubarwa ba a dalilin rufe boda ba ne ake noma shi. Abin da duniya ta sani shi ne kasa da kasa na yin huldar kasuwanci tun lokacin da Allah Ya halicci dan Adam sannan su ribatu da hakan. Amma gwamnatin ta tsuke kanta, ta hana kanta samun haraji daga kasuwanci ta kuma maida dan kasuwa marar sana’a wannan ba zai taimaka wa tattalin arzikin kasa ba. Ina amfanin rusa dan kasuwa ta karfafa manomi sannan idan manomin nan ya sayar da abincin da ya noma a karshe sai ya sayi sauran abubuwa da tsada duk kudin da ya samu su kare a nan. A duk tsarin tattalin arziki na duniya guda uku, na Dabid Ricardo ko Adams Smith abin da ake la’akari da shi shi ne wane tsari ne zai kawo walwala wato samun kudi. Babu dalili da za ka tilasta wa al’umma dole sai sun ci shinkafar Naira dubu 20 alhali ga ta dubu 10, Najeriya kasa ce ta kananan manoma da ke noma iya abin da za su ci, masu karfin su ne wadanda idan suka cire wanda za su ci ragowar idan suka sayar da ita za su yi sayayya da kudin. Idan ana rufe kan iyakar nan don tsaro ne ai an san yadda aka bi aka raba makaman nan a baya har da jiragen helikwafta an yi kamar yadda mazauna wasu kauyukan da lamarin ya shafa su ka rika bayyanawa.
Ana cewa sai da kasar China ta garkame iyakarta sannan ta samu ci gaba?
Ba haka Shugaba Mao ya yi ba, sai da ya tura jama’ar kasarsa zuwa kasashe daban-daban suka gano sirrin na’urorinsu na kimiyya da yadda aka yi su, suka dawo kasar suka kera su suka samu ci gaba. Mu kuma ko allura ba wanda muka tura ya koyo yadda ake yin ta, sai dai noma kadai. Wannan al’amari bai rasa nasaba da tunanin wadansu a kai, wanda a wannan zamani ba inda zai kai kasa kamar Najeriya. Tunda kasar nan ta kafu ba a taba yin tsadar abinci da ke hauhawa a cikin hanzari irin na wannan karo ba. Babban abin da ya jawo haka kuma shi ne manufofin gwamnati a kan musayar kudaden waje, kuma ba zai rasa nasaba da rashin daidaituwar ra’ayi tsakanin Shugaban kasa da Gwamnan Babban Banki ba. Dole ne Gwamnan Babban Banki ya zamo yana jin manufar Shugaban kasa. Haka dauke ofishin kula da tattalin arzikin kasa daga ofishin Shugaban kasa zuwa na Mataimakin Shugaban kasa bai dace ba, ya kamata ya ofishin Shugaban kasa yake kula da tsarin tattalin arzikin kasa kamar yadda yake kula da na tsaro aka samu nasara a yanzu. Da ma shi ne jama’a suka zaba ba mataimakinsa ba. Haka ya zama wajibi Shugaban kasa ya nemi mashawarta masu tausayin mutane, a duba tsarin tattalin arzikin nan a magance shi, sannan ya gaggauta sake kudin ’yan kwangila da aka rike domin samar da hada-hada ga tattalin arziki.