Sam Allardyce ya raba gari da Leeds United

Allardyce ya gaza ceto Leeds United daga nutsewa rukunin gasar Championship.

Sam Allardyce ya raba gari da Leeds United

Sam Allardyce ya raba gari da Leeds United bayan jagorantar kungiyar a wasanni hudu kafin ta nutse ta koma buga gasar Championship.

Mai shekaru 68 ,ya yi rashin nasara a wasa uku sannan ya buga canjaras a biyu bayan ya maye gurbin Javi Garcia a ranar 3 ga watan Mayu.

Leeds ta shafe kakar wasa uku a gasar Firimiyar Ingila kafin ta gamu da wannan cikas din.

“Na ji dadin jagorantar Leeds United, babbar kungiya ce mai magoya baya da dama,” in ji Allardyce.

Shugaban Leeds United Angus Kinnear ya ce “muna godiya ga Sam da namijin kokarin da ya yi domin taimakonmu.”

Ƙungiyar ta ce za ta sanar da sabon koci a makonnin da ke tafe.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba