Sama da mutum 100 suka musulunta a garin Ajakurama na Jihar Edo

Kimanin mutane dari ne tsakanin maza da mata har da yara suka shiga addinin Musulunci a cikin wannan makon a garin Ajakurama da ke Jihar Edo.Al’amarin ya wakana ne, a lokacin da malaman kungiyar Izalatul bidi’a wa’ikamatus sunna suka je garin, wanda wani Musulmi dan asalin garin mai suna Yakubu Janaral ya shige musu gaba […]

Sama da mutum 100 suka musulunta a garin Ajakurama na Jihar Edo
Sama da mutum 100 suka musulunta a garin Ajakurama na Jihar Edo

Kimanin mutane dari ne tsakanin maza da mata har da yara suka shiga addinin Musulunci a cikin wannan makon a garin Ajakurama da ke Jihar Edo.
Al’amarin ya wakana ne, a lokacin da malaman kungiyar Izalatul bidi’a wa’ikamatus sunna suka je garin, wanda wani Musulmi dan asalin garin mai suna Yakubu Janaral ya shige musu gaba suka je garin, suka yi wa’azi na Musulunci; wanda hakan ya jawo hankalin al’ummar garin, suka rika zuwa babu kama hannun yaro, suka ci gaba da karbar kalmar shahada.
Kamar yadda Ustaz Usman Alkanawi, daya daga cikin malaman kungiyar ya yi bayani, ya ce: “Hakika mun yi farin ciki kuma muna godiya ga Allah da wannan yunkurawan da muka yi zuwa wannan garin da kyakkyawar manufa, domin tun da farko mun samu labarin cewa akwai mutane da dama wadanda suke son su shiga addinin Musulunci a wannan garin na Ajakurama.
“Mun je wannan garin ta jagorancin wani dan garin wanda yake shi Musulmi ne mai suna Yakubu Janaral kuma mun samu nasara kuma malamai wadanda suka taimaka suka yi wa’azi, akwai malam Usman Aboki daga Jihar Delta da Malam Yusufa, sai Malam Nuruddini daga Aduwawa Benin da Malam Musa Usman. Sai malamai daga Abuja, Ustaz Husaini Yusufu Mabera da Malam Faruk Bello Amira da Malam Shehu Ibrahim tare da mai ja musu baki Alaramma Malam Mu’awiya daga Benin. Wannan wa’azin shi ne na farko da aka taba je musu na Musulunci a tarihin garin kuma ya yi tasiri a zukatansu matuka har suka mika wuya suka shiga Musulunci. Mun samu akalla mutum dari tsakanin maza da mata a garin wadanda suka musulunta.” Inji shi.