Sama da mutum 100 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kwara

Mutanen na kan hanyarsu ce ta dawowa daga wani biki

Sama da mutum 100 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kwara

Jirgin Ruwa

Sama da mutum 100, cikinsu har da wani magidanci da ’ya’yansa hudu ne aka tabbatar da rasuwarsu a wani hatsarin kwale-kwale a kauyen Egbu da ke Karamar Hukumar Patigi ta Jihar Kwara.

Lamarin, kamar yadda wakilinmu ya gano, ya faru ne ranar Litinin, lokacin da igiyar ruwa ta kada jirgin da suke ciki ya kuma je ya daki wata bishiya.

Mutanen dai na kan hanyarsu ce daga wani kauye mai suna Egboti a Jihar Neja.

Kimanin gawarwakin mutum 50 ne aka iya ganowa tun bayan faruwar hatsarin.

Wasu majiyoyi daga kauyen sun shaida wa wakilinmu cewa mamatan sun taso ne daga kauyen Kpada.

Majiyar ta kuma ce, “Jirgin na dauke ne da sama da mutum 300 a cikinsa kuma sun dawowa ne daga wajen wani biki.

“Mutum 69 daga cikin wadanda suka rasu sun fito ne daga Egbu, 36 daga Gakpan, sai kuma hudu daga kauyukan Kpada da ke Karamar Hukumar Patigi. An kuma ceto sama da 75 daga cikinsu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar hakan.

Sai dai ya ce ba su da cikakkun bayanai, amma ya ji an ce sama da mutum 100 sun rasu, inda ya yi alkawarin ba da cikakken bayani a kan haka da zarar ya samu.

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC