Sama da mutum 27 aka kona a harin kauyukan Katsina
Sama da mutum 27 ne aka kone kurmus a kauyen Tsauwa yayin da har yanzu ana cikin aikin binciko wasu daga cikin buraguzan kasa da kuma wasu da har yanzu ba’a san halin da suke ciki ba. Ƴan bindigar da ake zargin sun kawo harin ramuwar gaiya wadanda suka zo akan babura 150 dauke da […]
Sama da mutum 27 ne aka kone kurmus a kauyen Tsauwa yayin da har yanzu ana cikin aikin binciko wasu daga cikin buraguzan kasa da kuma wasu da har yanzu ba’a san halin da suke ciki ba.
Ƴan bindigar da ake zargin sun kawo harin ramuwar gaiya wadanda suka zo akan babura 150 dauke da mutum 3 akan kowane babur da kuma motar Kanta, an ce sun shigo garin ne a lokacin da mutanen garin ke sallar magariba.
“Sun shigo garin ne tare da bankawa garin wuta wadda ta cinye akalla kashi 90 cikin 100 duk da alamu sun nuna kamar an yi zaben gidajen da aka kona ne.
Mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu dai mata ne, tsofaffi da kananan yara tare da dabbobi da kayan abinci.
Kamar yadda Kwamishinan Ƴan sanda CP Sanusi Buba, ya ce ana zargin maharan sun fito daga dajin Zamfara ne. Ƴan bindigar wadanda suka fara shiga garin Dankar sun kashe mutum 9, amma wata majiyar daga mutanen garin sun ce mutum 11 ne.
A wani rahoto, rundunar ƴan sandan tayi nasarar kama wani mutun da ya kawo Awaki a cikin garin Katsina domin ya sayar daga wancan yanki da aka kai wannan hari a washegarin kai wancan hari, wanda rundunar ke tuhumarsa akai.
Kazalika, rundunar ƴan sandan hadin gwiwa da jami’an sojojin da suka kai dauki sun yi nasarar kama babura 9, wadanda su ma ana cikin bincike.