Sama da mutum 4000 ke dauke da kanjamau a Jihar Nasarawa – Hukumar NASACA
Hukumar Yaki da Cutar kanjamau ta Jihar Nasarawa (NASACA) ta ce kawo yanzu, bincike na musamman da ta gudanar ya gano cewa mutum 4, 245 ne ke dauke da cutar a jihar. Babbar Daraktar Hukumar Dokta Ruth Adabe ce ta sanar da haka a jawabinta wajen wani taron kara wa juna sani na wuni daya […]

Hukumar Yaki da Cutar kanjamau ta Jihar Nasarawa (NASACA) ta ce kawo yanzu, bincike na musamman da ta gudanar ya gano cewa mutum 4, 245 ne ke dauke da cutar a jihar.
Babbar Daraktar Hukumar Dokta Ruth Adabe ce ta sanar da haka a jawabinta wajen wani taron kara wa juna sani na wuni daya da Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) ya shirya wa ’yan jarida da shugabanninsu kan hanyoyin wayar da kan al’ummar jihar domin kare yaduwar cutar daga uwa zuwa danta da kuma tallafa wa matasa, wanda aka gudanar a garin Keffi da ke jihar a karshen makon jiya.
Dokta Ruth, wacce Dokta Peter Attah ya wakilta a wajen taron, ta ce a halin yanzu mutum 2,550 cikin wadanda ke dauke da cutar suna shan magunguna, inda a cewarta, kashi 10 daga cikin wadanda ke dauke da cutar a jihar matasa ne.
Ta bayyana fargaba dangane da yadda a halin yanzu ake fuskantar karancin magungunan da ake bai wa masu dauke da cutar a jihar, sakamakon rashin tallafi, musamman na kudi daga cibiyoyin agaji da gwamnatoci a dukan matakai.
Sai ta jinjina wa Asusun UNICEF game da bullo da muhimman hanyoyin tallafawa wajen yaki da yaduwar cutar a jihar da kasa baki daya, musamman ta shiryawa da gudanar da taron bitar a jihar.
A nasa jawabin, Shugaban Sashin Watsa Labaru na Asusun UNICEF a Jihar Kaduna, Rabi’u Musa ya bayyana cewa taron wata hanya ce ta aiwatar da shirin tallafa wa cibiyoyin da ke fafutikar kare yaduwar cutar da tallafa wa masu cutar a jihar, kamar yadda aka tsara a shirye-shiryen hukumar a Jihar Nasarawa na shekarar 2019. Ya kara da cewa shirin yana samun tallafin gwamnatin Jihar Nasarawa wajen tabbatar da aiwatar da shi.
Daga nan sai ya bukaci ’yan jarida a jihar, wadanda suka halarci taron da wadanda ba su halarta ba, su mai da hankali ga batutuwan da suka shafi kula da lafiya da harkokin matasa, su kuma rika rubuta labarai ko rahotanni a kai-a-kai domin wayar da kan al’ummar jihar da kasa baki daya, don karewa tare da dakatar da yaduwar cutar a jihar baki daya.