Sama da mutum dubu 20 ke fama da ciwon suga a Sakkwato

A Jihar Sakkwato akwai sama da mutum dubu 20 da ke fama da ciwon siga wadanda suka yi rajista da kungiyar masu fama da cutar ta kasa reshen jihar Jami’in kiwon lafiya kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Ciwon Suga reshen jihar, Muhammad Wakili Dange ne ya bayyana haka a wurin taron wayar da kai kan abincin […]

Sama da mutum dubu 20 ke fama da ciwon suga a Sakkwato

Rakiya Kilgori a dama da Hajiya Salamatu a hagu

A Jihar Sakkwato akwai sama da mutum dubu 20 da ke fama da ciwon siga wadanda suka yi rajista da kungiyar masu fama da cutar ta kasa reshen jihar

Jami’in kiwon lafiya kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Ciwon Suga reshen jihar, Muhammad Wakili Dange ne ya bayyana haka a wurin taron wayar da kai kan abincin da masu fama da ciwon suga za su rika ci daidai gwargwado ba sai sun wahalar da kansu ba, wanda daya daga cikin jagororin kungiyar Hajiya Rakiya Garba Kilgori ta shirya na wuni daya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato.

Wakili Dange wanda tsohon ma’aikacin asibiti ne ya jinjina wa wadda ta shirya taron, inda ya yi fata mahalarta za su fahimci abin aka fada musu kuma su sanya shi a aikace don kare lafiyarsu.

Ya ce bincike ya gano cewa mai ciwon suga yana iya cin komai, “Amma ba da yawa ba, amma abinci mai dusa kuwa ana son ya ci ba tare da an cire dusar ba. Kayan marmari ma ya guji shan masu zaki da yawa kamar ayaba da kankana da abarba. Ciwon ana iya warkewa amma ba gaba daya ba sai dai ka rika rayuwa kamar kowa, abin da ake so a nan yadda za a rika kare hadarin ciwon domin yana makantar da mutum ko rasa wani bangare na jiki ko samun hawan jini. Mai ciwon dole ya rika shan magani da motsa jiki da cin abinci. Duk wanda ya rike wannan ciwon ba zai masa lahani ba,” inji shi.

Daya daga cikin jagororin kungiyar a Sakkwato da Najeriya kuma mamba a kungiyar Blue Circle Boices ta Duniya, Hajiya Rakiya Garba Kilgori ce ta shirya taron domin sanar da masu fama da ciwon irin abincin gida da za su rika ci.

Kilgori ta ce, “Can baya gadon ciwon ake yi amma yanzu ba haka ba ne, karamin yaro ko yarinya ’yan shekara 14 sai a gansu da ciwon. Dole ne mu tashi tsaye mu fadakar kan abincin gida da mai ciwon zai iya ci bai yi masa lahani ba.”

Hajiya Salamatu jami’ar lafiya ce da ke da ilimin abincin, kuma tana fama da ciwon na tsawon shekara 32, ta yi kira ga masu ciwon su bar shan maganin gargajiya domin ba ya aiki. Sannan ta ce su bar shan kayan zaki.