‘Sama da mutum miliyan 4 sun tsere daga Ukraine saboda yaki’
An kuma jikkata dubban mutane tun bayan da Rasha ta mamaye kasar
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan hudu ne suka tsere daga kasar Ukraine, tun bayan da Rasha ta kaddamar da hare-harenta a kasar.
Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce sama da ’yan gudun hijira miliyan hudu ne suka tsere daga kasar tun ranar 24 ga watan Fabrairu.
- Magoya bayan Super Eagles sun yi ajalin likita dan kasar Zambiya a Abuja
- Ficewar Kwankwaso: PDP ta rushe shugabancinta a Jihar Kano
Daga cikinsu, mutum miliyan 2.3 ne suka shiga makwabciyar kasar ta Poland don neman mafaka.
Kimanin mutum miliyan 6.5 ne kuma aka raba su da gidajensu a cikin Ukraine din.
A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta ba da rahoton mutuwar fararen hula 1,179 a Ukraine a dalilin hare-haren Rasha.
A cewar Ofishin kare hakkin bil Adama na Majalisar, tun lokacin da Rasha ta fara mamayar Ukraine an kuma an jikkata kimanin mutum 1,860.
“Yawancin fararen hular abun ya shafe su ne ta hanyar amfani da makamai masu fashewa da ke da tasirin gaske, ciki har da harsasai daga manyan bindigogi da na’urorin harba rokoki da harba makamai masu linzami da na sama,” inji sanarwar.