Sama’ila ya yi ayyuka da dama a mazabar Jos da Bassa – Murtala Mamsa
Daraktan Yakin Neman Zaben Alhaji Sama’ila Muhammad Abdullahi a Majalisar Tarayya daga mazabar Jos ta Arewa da Bassa a Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar ADC na karamar Hukumar Bassa, Malam Murtala Abdullahi Musa (Mamsa), ya ce dan takararsu ya yi ayyuka da dama na raya al’umma a mazabar lokacin da ya wakilce su a shekarar […]
Daraktan Yakin Neman Zaben Alhaji Sama’ila Muhammad Abdullahi a Majalisar Tarayya daga mazabar Jos ta Arewa da Bassa a Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar ADC na karamar Hukumar
Bassa, Malam Murtala Abdullahi Musa (Mamsa), ya ce dan takararsu ya yi ayyuka da dama na raya al’umma a mazabar lokacin da ya wakilce su a shekarar 2007 zuwa 2011.
Malam Murtala Abdullahi Mamsa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce ayyukan da Sama’ila ya yi sun fi na duk wadanda suka rike wannan kujera tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999.
Ya ce Alhaji Sama’ila ya giggina rijiyoyin burtsatse a yankunan mazabar tare da ba mata 20 daga kowace mazaba rancen jarin kama sana’o’i. Sauran su ne ba shugabanni da sarakuna motoci tare da raba wa daruruwan matasa rancen babura.