Samar da ababen more rayuwa su ne ke gaban gwamnatocin APC -Asiwaju Bola Tinubu
Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo cikin jam’iyyar APC (All Progressibe Congress), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce samar da ababen more rayuwa su ne kan gaban jam’iyyarsu.Asiwaju Bola Tinubu ya fadi haka ne a yayin da yake magana a garin Imoru-Ijebu da ke Jihar Ogun sa’ilin da ake bikin nadin sarautar gargajiya ga shugaban […]
Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo cikin jam’iyyar APC (All Progressibe Congress), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce samar da ababen more rayuwa su ne kan gaban jam’iyyarsu.
Asiwaju Bola Tinubu ya fadi haka ne a yayin da yake magana a garin Imoru-Ijebu da ke Jihar Ogun sa’ilin da ake bikin nadin sarautar gargajiya ga shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Bisi Akande.
Ya ce wannan dabi’a ita ce jigon nasarar gwamnatinsa a lokacin da yake mulki, lamarin da ya sa a su shida, shi kadai ne ya sake komawa kan karagar mulki, don haka ya yi kira ga wadanda da suka samu damar rike karagar mulki su nuna gaskiya da rikon amana don su samu nasarar sauke nauyin da Allah Ya dora musu.
Tsohon gwamnan ya ce cika alkawari shi ne sanin makamar mulki, kuma wannan zai sa kowane shugaba ya yi nasara, musamman kuma in ya kasance jama’ar da yake shugabanta su ne fifikon abin da ya sa gaba wajen kyautata rayuwarsu.
Dangane da cigaban Najeriya gaba daya, sai Asiwaju Bola Tinubu ya ce ko ’yancin fadin albarkacin baki ma da aka samu wani cigaba ne, amma dai yanzu mutane sun sa ido su ga me gwamnati za ta sama musu na more rayuwa.