Samar da aiki ga matasa ne maganin matsalolin Najeriya – Dokta Mai Abba

Mataimakin Shugaban kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) kuma shugaban kamfanin mulmula wayoyin lantarki na ALIND da ke Bauchi, Dokta Ahmad Mai Abba, ya ce samar wa matasa aikin yi ne babbar hanyar magance matsalolin Najeriya. Dokta Mai Abba ya bayyana haka ne lokacin da kungiyar dalibai ’Yan Asalin Jihar Bauchi (NUBASS) reshen Jami’ar Abubakar […]

Samar da aiki ga matasa ne maganin matsalolin Najeriya – Dokta Mai Abba
Samar da aiki ga matasa ne maganin matsalolin Najeriya – Dokta Mai Abba

Mataimakin Shugaban kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) kuma shugaban kamfanin mulmula wayoyin lantarki na ALIND da ke Bauchi, Dokta Ahmad Mai Abba, ya ce samar wa matasa aikin yi ne babbar hanyar magance matsalolin Najeriya.

Dokta Mai Abba ya bayyana haka ne lokacin da kungiyar dalibai ’Yan Asalin Jihar Bauchi (NUBASS) reshen Jami’ar Abubakar Tafawa balewa suka ba shi lambar yabo kan kokarinsa na inganta manya da kananan masana’antu da kuma ci gaban matasa.
Dokta Ahmad Mai Abba wanda ya yaba wa kungiyar daliban da lura ya bukaci su kasance masu taimakawa wajen gina kasa ba rusa ta ba, kuma ya shawarci shugabanni kan su lura da irin taimakon da aka yi musu a baya wajen ba su ilimi kyauta da ba su aiki ba tare da wata matsala ba, ta hanyar sauya rayuwar matasa don sune shugabannin gobe. Ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da matasa a yanzu a wajen lalata harkokin tsaro da siyasa da zamantakewa, inda ya ce ko dai a kyautata makomar Najeriya ta hanyar nuna jagoranci nagari da yin amfani da dukiyar kasa wajen bayar da ilimi mai inganci kyauta ga matasa da kuma ba su jari ko ayyukan yi a duk lokacin da suka taso domin barinsu kara zube ke sa su aikata laifi.
Ya bukaci gwamnati ta bayar da jarin kafa masana’antu da farfado da wadanda suka durkushe don samar da aikin yi ga jama’a. Kuma ya shawarci shugabannin su dauki shawarar da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya bayar ga Jonathan don a gyara matsalolin Najeriya.
Shugaban kungiyar ta NUBASS Adamu Jibrin Gyara ya ja hankalin shugabanni kan su himmatu wajen gyara rayuwar matasa don a samu tsarkake al’umma.