‘Samar da aikin yi ga jama’a na daga nasarorin da kungiyarmu ta samu’
Shugabannin kungiyar masu bunkasa al’adun gargajiya da ke otel din Eko a jihar Legas sun bayyana cewa sun kafa kungiyarsu ne don su magance zaman kashe wando a tsakanin al’umma.A ganawarsa da Aminiya a harabar ofishin kungiyar da ke farfajiyar otel din, daya daga cikin dattaawan kungiyar, Alhaji Muktar Adam Tofa ya ce samar da […]
Shugabannin kungiyar masu bunkasa al’adun gargajiya da ke otel din Eko a jihar Legas sun bayyana cewa sun kafa kungiyarsu ne don su magance zaman kashe wando a tsakanin al’umma.
A ganawarsa da Aminiya a harabar ofishin kungiyar da ke farfajiyar otel din, daya daga cikin dattaawan kungiyar, Alhaji Muktar Adam Tofa ya ce samar da aikin yi na daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu zuwa yanzu.
“kwazon da mu mutanen Arewa muka nuna na baro Arewa mu zo Legas mu dunkule wuri daya don mu yi maganin zaman banza wata babbar nasara ce a gare mu da kungiyarmu baki daya. Domin har gobe duk lokacin da samu bako daga Arewa da ba shi da abin yi, muna kama masa wurin da zai zauna ya rika sana’a yana ciyar da iyalansa. Ka ga shi ma wannan wani babban ci gaba ne,” in ji shi.
Ya kara da cewa jabun kayayyaki da wasu mutane suke yi a yanzu yana janyo musu cikas. Ya ce burin kungiyar shi ne ta samu wurin da yake mallakarta ne don ci gaba da gudanar da kasuwancin ’ya’yanta.
Alhaji Muktar ya ce ba su fuskantar kyama daga wurin jama’a saboda sayar da kayan gargajiya da suke yi.
Mataimakin Shugaban kungiyar Sani Hasan danjuma, ya ce sun kafa kungiyar ne saboda su yi magana da murya daya idan wata matsala ta bijiro.
Ya bayyana matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya kamarsu rashin ciniki da kuma rashin samun tallafi daga gwamnati. A karshe ya yaba wa shugabannin kungiyar saboda kyakkyawan jagorancin da suke dorata a kai da kuma membobinta saboda yadda suke wa shugabanin biyayya.