Samar da ingantaccen ilimi ga mata ne tushen ginin al’umma – Amina Makintami

Hajiya Amina Makintami ita ce Shugabar Makarantar ’Yan Mata ta Maiduguri, ta shahara a Jihar ta Borno da wasu jihohi makwabta kan bada gudunmawarta a harkar ilimi. Kuma ita ce mace ta farko a Maiduguri da ta bude makaranta mai zaman kanta mai suna Innobatibe School shekara 20 da suka shige. Aminiya ta tattauna da […]

Samar da ingantaccen ilimi ga mata ne tushen ginin al’umma – Amina Makintami

Hajiya Amina Makintami, Shugabar Makarantar ’Yan Mata ta Maiduguri

Hajiya Amina Makintami ita ce Shugabar Makarantar ’Yan Mata ta Maiduguri, ta shahara a Jihar ta Borno da wasu jihohi makwabta kan bada gudunmawarta a harkar ilimi. Kuma ita ce mace ta farko a Maiduguri da ta bude makaranta mai zaman kanta mai suna Innobatibe School shekara 20 da suka shige. Aminiya ta tattauna da ita a kan hobbasar da take na ganin mata sun samu ilimi, inda ta ce ba mata ingantaccen ilimi ne tushen ginin ilimi:

Tarihina

An haife ni a ranar 2 ga Mayu 1962 a  garin Hawul, Karamar Hukumar Hawul a Jihar Borno. Na fara karatun firamare ta Shaffa Central, bayan na kammala a 1974 na shiga makarantar Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Maiduguri, inda na gama a 1979.

Allah cikin ikonSa a shekarar na samu gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri, inda na kammala a 1984, na samu digiri a fannin ilimi (Education). Bayan na yi wa kasa hidima, sai na fara aiki da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno.

Shekara biyu bayan nan, sai na sake komawa Jami’ar Maiduguri na yi digiri na biyu shi ma a fannin ilimi. Bayan na dawo sai aka ba ni Mataimakiyar Shugabar Makarantar ’Yan Mata ta Konduga, ina Konduga a 1992 sai aka dawo da ni Makarantar Birgediya Maimalari a nan Maiduguri na zama Mataimakiyar Firansifal Bangaren Mulki, har dai ta kai na zama Shugabar  Makarantar a shekarar 2006. A yanzu haka ni ce Shugabar Makarantar ’Yan Mata ta Maiduguri.

Ilimin mata yana samun koma baya

A gaskiya ganin yadda ilimin mata ya samu nakasu a wannan shiyya tamu ta Arewa maso Gabas hakan na daya daga cikin abubuwan da a kullum suke ci mini tuwo a kwarya, ganin na tashi cikin gidan ilimi, domin mahaifina malamin makaranta ne, wanda hakan ya sa na tashi ina da kishin yin karatu, kuma in bada gudunmawata a kan harkar bunkasa ilimi a Jihar Borno da kasa gaba daya. Ina Shugabar Makarantar Maimalari ce, yawan bukatun jama’ar unguwa suka fara neman a bude makarantar da za a rika koyar da ’ya’yansu, domin su samu ilimi mai nagarta. Allah cikin ikonSa a 1999 na samu damar bude makaranta da burin ba ilimin ’ya’ya mata fifiko, kuma a yau shekara 20 babu abin da za mu ce, sai godiya. Domin ina bada tallafi ga karatun ’ya’ya mata da kuma yara marasa galihu. Kuma ina alfahari da irin daliban da na karantar.

Kalubale

Babban kalubalen da na fuskanta, shi ne yadda ’yan Boko Haram suka kona mana makaranta da kwamfutoci fiye da 100  wadanda Ministan Ilimi ya ba mu, a wannan Makaranta ta Innobatibe. Na biyu kuma suka sake zuwa ana karatu da rana suka kashe iyayen dalibai da suka zo daukar ’ya’yansu, da mai gadi da kuma malaminmu, har da dalibai. To a gaskiya wannan al’amarin ya ba ni tsoro sosai, akwai lokacin da muka rufe makarantar, bayan da ’yan Boko Haram suka saka sake zuwa mana, suka kashe wani mutum da ya zo daukar ’ya’yan maigidansa, kuma suka kone shi a nan gaban makarantar, amma dai  duk wannan bai hana mu ci gaba da gudanar da makarantar ba, bisa taimakon al’umma da kuma kulawar gwamnati.

Sai kuma wani mutum da ya zo ya nemi maida wannan aiki namu  baya, bayan da gwamnati ta ba mu fili, sai ya zo ya ce ai filin gonar kakansa ce, inda ya kai ni kotu, kusan ya kai ni kotu har hudu, duk ina samun nasara. To hakika dogon lokacin da aka diba ana shari’ar ya kawo tsaiko, domin mun shafe shekara 12 muna shari’a.

Hajiya Amina da Adanta a tsakiya da kuma mijinta a dama
Hajiya Amina da Adanta a tsakiya da kuma mijinta a dama

Nasarori

An samu nasarori da dama ganin yadda muka fara gudanar da wannan makaranta a gidan haya, amma cikin shekara daya, sai Gwamnatin Jihar Borno ta wancan lokacin a mulkin marigayi Gwamna Mala Kachalla, ganin yadda muke bada kula ga ilimin ’ya’ya mata, ya kuma gamsu da hakan, sai ya bada umarnin a ba mu babban fili, wanda muka gina matsuguni na dindindin, kuma alhamdulillahi mun gode wa Allah, ta kowane fannin a rayuwa mun samu nasara. Domin ina tafiyar da makaranta irin wannan ga kuma shugabanci wata makarantar da nake yi, ka ga sai godiya.

Tallafi

A yanzu haka muna kokarin bude wata gidauniya da za ta rika kula da duk yaran da muka lura ba su da damar yin karatu, kuma suna da sha’awar yin karatun. Ita wannan gidauniya da za mu bude za ta fi bada kula ga ilimin ’ya’ya mata, duk da yake dama akwai wannan akwai tanadi, amma yanzu ana son a fadada abin ya game kowa ne, musamman ganin yadda yara ke gararamba a kan titi. Wadanda ya kamata a ce suna makaranta ne amma abin takaici, idan ka gan su, sai ka yi hawaye. To na kudiri aniyar tabbatar da ganin na yi wani abu da zan bari ana tunawa da ni. Shi ya sa idan na ga irin wadannan yara nakan duba, idan ya dace in kai su makarantar gwamnati sai in dauke su, in kai su. Idan kuma makaranta mai zaman kanta ce ta kamace su, sai in dauke su a nan makarantar.

Burina

Babban burina in bar tushen ilimi mai inganci a tsakanin al’umma, domin samar wa yara ilimi babu abin da ya fi shi. Wannan shi ne burina, ganin ina mu’amala da ’yan mata da na karantar da su, na kula da kuma tarbiyyarsu. Duk wannan abu ne da idan ka ba su kulawa to ka gina al’umma, don in ka ba mace daya ilimi tamkar ka ba wa al’umma gaba daya ne, saboda haka babban burina in bar tushen da na  dasa na ilimi in ga ana ci gaba da morarsa a tsakanin al’umma.

Shawara ga iyaye

Shawarata ga iyaye ita ce, mu tuna wannan aiki hakki ne a kanmu, musamman mu iyaye mata. Don haka dole ne, iyaye mata mu tashi tsaye mu ba yaranmu ilimi. Ni dai a kullum bukatata ke nan. Iyaye mata mu ne kullum muke gida, kada mu yarda da son tara abin duniya wajen dora wa yara tallace-tallace. In muka bada karfin wajen neman ilimi, to wallahi ba mu da wata matsala. Amma idan mu iyaye muka yi watsi da kula da ilimin ’ya’yanmu, to gaskiya za mu ci gaba da samun matsala. Sannan wajibi ne iyaye su rika duba yadda karatun ’ya’yansu yake tafiya, ta bincikawa wacce irin makaranta ka sa danka, walau ta gwamnati ce, ko mai zaman kanta. Sannan mu iyaye mu rika sa ido a kan wadanne irin abokai ko kawaye ’ya’yanmu suke mu’amala da su. Domin Allah Zai tambaye mu a kansu. Sannan harkar  ilimi ba gwamnati kadai za mu bar wa nauyinta ba, dole ne, mu iyaye mu rika bada tamu gudunmawar wajen ci gaban ilimi.

Abinci da kayan sawa

Ina cin kowane irin abinci, amma na fi son tuwon masara da miyar kubewa. Kaya kuwa kowane na samu sawa nake yi.

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara