Samar da kayan aiki ga jami’an tsaro ya fi tsawaita dokar ta-baci – Kwamishina
Kwamishinan Ilimi na Jihar Yobe Alhaji Muhammad Lamin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta samar wa jami’an tsaron da aka tura jihohin da aka sa musu dokar ta-baci ingantattun kayan aiki da za su iya fuskantar kalubalen mahara, maimakon tsawaita wa’adin dokar ta bacin.Alhaji Muhammad Lamin ya bayyana haka ne a a tattauanwarsu da Aminiya a […]

Kwamishinan Ilimi na Jihar Yobe Alhaji Muhammad Lamin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta samar wa jami’an tsaron da aka tura jihohin da aka sa musu dokar ta-baci ingantattun kayan aiki da za su iya fuskantar kalubalen mahara, maimakon tsawaita wa’adin dokar ta bacin.
Alhaji Muhammad Lamin ya bayyana haka ne a a tattauanwarsu da Aminiya a Damaturu kan cece-kucen da ake yi game da kara wa’adin dokar a jihar da sauran jihohin da suke cikin halin tabarbarewar tsaron.
Alhaji Lamin ya ce kiran da wasu mutane ke yi na neman a kara wa’adin dokar ta-bacin a jihohin Yobe da Borno da Adamawa ba ita ce mafita ba, mafitar ita ce a samar wa jami’an tsaron makamai masu inganci da suka dara na ’yan tada kayar baya.
Da ya koma bangaren ilimi sai ya ce gwamnatin jihar ta fi mayar da hankali ne kan abin da ya shafi gina sababbin ajujuwa da gyara wadanda suka lalace da horar da malamai dabarun koyarwa don dacewa da bukatun tsarin ilimi na kasa.
Ya nanata kudirin gwamnatin jihar na samar da kayayyakin aiki masu nagarta ga dukan makarantun jihar don ci gaban ilimi.