‘Samar da masana’antu a kudancin Kaduna zai dakile fitina a yankin’
kungiyar Citizen Monitoring Group ta shirya wani taron zaman lafiya ga masu ruwa-da-tsaki a Kudancin Kaduna domin dorawa kan taron zaman lafiya da ta gudanar a watan Yulin da ya gabata. A lokacin da yake bayyana makasudina taron, shugaban ayarin, Rabaran Gideon Para-Mallam daga Jos, ya bayyana cewa sakamakon zaman farkon an cimma matsayar sake […]

kungiyar Citizen Monitoring Group ta shirya wani taron zaman lafiya ga masu ruwa-da-tsaki a Kudancin Kaduna domin dorawa kan taron zaman lafiya da ta gudanar a watan Yulin da ya gabata.
A lokacin da yake bayyana makasudina taron, shugaban ayarin, Rabaran Gideon Para-Mallam daga Jos, ya bayyana cewa sakamakon zaman farkon an cimma matsayar sake shirya wannan taro, amma ga masu ruwa-da-tsaki da suka kunshi daidaikun masu fada-a-ji da wakilan kungiyoyi.
A jawabin Mataimakin Shugaban kungiyar Masu Masana’antu ta kasa (MAN), Mista Jonathan Onigbinde, ya ce yadda yankin Kudancin Kaduna ke da albarkatun kasa da na noma, samar da masana’antu a yankin na daga cikin abubuwan da za su dakile yawan tashin hankali a yankin. “Sai dai kuma hakan ba zai taba yiwuwa ba in zaman lafiya bai samu a yankin ba. Amma yayin da kowa ya tabbatar yana da hannun jarinsa a wata masana’anta ko wata harka ta arziki da yake juyawa ba zai so wani ko wadansu su zo su ruguza masa tattalin arzikinsa ba,” inji shi.
Mista Onigbinde, ya ce abin takaici ne irin biliyoyin Nairan da Najeriya ke kashewa wajen shigo da abinci daga kasashen waje, alhali ya kamata zuwa yanzu a ce Najeriya tana fitar da abinci ne zuwa wasu kasashe. “Muna fata nan gaba kadan Najeriya za ta fara fitar da abinci zuwa wasu kasashen ketare sai dai kafin nan, dole sai mun fara samar da abincin tukuna,” inji shi.
Shi kuwa tsohon dan Majalisar Wakilai na mazabar Jama’a da Sanga, Honorabul Ado Dogo Audu ya yi kira ne ga mahalarta taron kan su yi watsi da jita-jita da kalmomin batanci a tsakanin abokan zamansu. “Gwamnati tana kashe makudan kudaden da suka kamata ta yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan ci gaba a ayyukan kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsaro,” inji shi.
Sai ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kaduna ta bude manyan makarantun da suke rufe a yankin tun lokacin rikice-rikicen da suka auku a karshen bara zuwa farkon bana.
An bayar da dama ga mahalarta taron su bayyana abin da suke ganin shi ne ke hana ruwa gudu da kuma haifar da yawan tashe-tashen hankulan da suke faruwa a yankin, inda mutane daga bangarori da dama suka tofa albarkacin bakinsu, a karshe suka bukaci jama’a su kawo matsalolin da kuma mafita kan yadda za a shawo kansu a rubuce saboda karancin lokaci.
Shugabannin tsaro da suka hada da sabon shugaban ’yan sandan yankin, (Eriya Kwamanda), ACP Kayode Sunday da takwararsa na sojoji, Kanar I. Ekpenyong sun gargadi jama’a su zamo masu kiyaye hakkin zamantakewa tare da gaggauta sanar da su duk wani abu da ba su yarda da shi ba cikin gaggawa.
Shugabannin kungiyoyin Jama’atu Nasril Islam da takwararta ta Kiristoci (CAN) suna daga cikin mahalarta taro.