Samar da motocin noma zai kara habaka tattalin arzikin Najeriya – Sarkin Noma
Aminiya: A matsayin ka na manomi kuma Sarkin Noman Jihar Kano, ya ya kake ganin tsarin aikin gona musamman ganin yadda kasar nan take canzawa ta wannan fanni? Sarkin Noma: To da farko dai kafin in ce wani abu ya na da kyau in fara nuna godiyar manoman Najeriya bisa yadda gwamnatin tarayya da na […]
Aminiya: A matsayin ka na manomi kuma Sarkin Noman Jihar Kano, ya ya kake ganin tsarin aikin gona musamman ganin yadda kasar nan take canzawa ta wannan fanni?
Sarkin Noma: To da farko dai kafin in ce wani abu ya na da kyau in fara nuna godiyar manoman Najeriya bisa yadda gwamnatin tarayya da na jihohi suka fara daukar kyawawan matakai na bunkasa aikin gona a wannan kasa tamu. Sannan ina fata dukkanin shirye-shiryen da ake bullowa da su na bunkasa noma za su cigaba da samun kulawa ta musamman ta yadda al’amura za su kara inganta.
Batun tsare-tsaren aikin gona da ake yi a wannan kasa tamu kuwa sai in ce kwalliya ta na biyan kudin sabulu, domin duk inda ka duba zaka ga cewa damina ta yi kyau saboda tsayawa da aka yi wajen samar da kayan aikin noma kamar su taki da magungunan feshi da kuma kyawawan irin shukawa, wanda hakan yana nunar da cewa Najeriya zata zamo a sahun farko wajen dogaro dakai ta fuskar samar da abinci a nahiyar mu ta Afirka.
Aminiya: A wannan shekarar gwamnatin tarayya tare da hadin gwuiwar jihohi ta samar da takin zamani ga manoma kuma a farashi mai sauki, ya ya ka ga wannan tsari musamman ganin cewa ba a saba yin irin sa ba a baya?
Sarkin Noma: Babu shakka wannan tsari ya yi mana dadi kuma mun yi godiya da yadda aka fahimci cewa samar da wadataccen taki ga manoma shi ne mafi amfani muddin dai da gaske ake yi wajen bunkasa sana’ar noma a kowace kasa ta duniya, don haka ya na da kyau a ci gaba da wannan tsari saboda alamu suna nuna cewa nan gaba kadan takin zamani zai wadata a kowane lungu da sako na fadin kasar nan kamar sauran abubuwa na bukatun yau da kullum.
Sai dai akwai bata gari wadanda suka soma yin zagon kasa ga wannan shiri na samar da taki ga manoma cikin sauki, inda suke gurbata takin da gwamnatin tarayya ta samar domin su ci kazamar riba. Wannan abin takaici ne kuma masu irin wannan halayya sun nuna cewa ba su so talaka manomi ya sami ingantattun kayan aikin gona cikin sauki.
Don haka mu manoma muna kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da jihohi da su fara daukar matakai na toshe kofofin ire-iren wadancan mutane bata-gari masu yi wa shirin wadata kasa da abinci zagon kasa, sannan mu kuma manoma za mu dauki namu matakai na dakile ayyukan masu gurbata kayan aikin noma ta hanyoyi da yawa wadanda ba zamu bayyana su ta kafafen yada labarai ba.
Samnan akwai bukatar a sanya idanu sosai domin magance yawaitar shigar jabun magungunan feshi cikin kasuwannin kasar nan da kuma sauran guraren da ake sayar da su domin tabbatar da cewa ana sayar da ingantattun magunguna a dukkanin guraren da ake kasuwancin su wanda yin hakan zai kawar da marasa gaskiya a sana’ar sayar da magungunan kwari insha Allahu.
Aminiya: Ko akwai wasu karin abubuwa da kuke ganin cewa idan aka aiwatar da su za a kara samun nasarori wajen bunkasa aikin gona a kasar nan?
Sarkin Noma: Lallai akwai muhimman abubuwa da idan aka yi su ko shakka babu noma zai zamo abin alfahari a kasar nan, sannan kowane manomi zai rubanya akinsa na noma rani da damina musamman ganin cewa yanzu gwamnatocin jihohi da ta tarayya sun bijiro da tsare-tsare domin ganin kasar ta rage karfin ta na dogaro da albarkatun man fetur.
Aminiya: Wadanne abubuwa kenan kake bukatar ayi domin kara karfafa maku gwiwar cigaba da noman rani da damina kamar yadda ka fara bayyanawa?
Sarkin Noma: Idan gwamnati ta fara aiwatar da shirin samar da motocin noma ga manyan manoma, to na hakikance za a ga yadda manoman za su yi aiki don ganin kasar nan ta kara habaka noman abinci kamar dai yadda muke gani a kasashen duniya da suka ci gaba ta fannan noma.
Sannan su kuma matsakaitan manoma sai a ba su shanun noma da garma domin su bunkasa ayyukan su na noma kana su kuma kananan manoma sai a samar masu da wani tallafi na kudade wanda za su fadada noman da suke yi kuma in Allah Ya yarda cikin shekaru uku zuwa hudu za a ga yadda noma zai bunkasa a kowane bangare na wannan kasa tamu mai albarka.
Aminiya: Ana korafin cewa idan aka baiwa manoma tallafin kudade a matsayin rance ba sa biya, me zaka ce dangane da wannan korafi?
Sarkin Noma: Gaskiya ne cewa wasu manoma suna kin biyan basussukan da aka ba su walau a gwamnatance ko kuma daga wasu cibiyoyi, amma na tabbata idan aka yi wani tsari ingantacce tare da sanya idanu kan ayyukan da suke yi kowa zai biya bashin da ya karba kuma ba tare da tsaiko ba, sannan daga karshe nake isar da sakona na fatan alheri ga daukacin manoman kasar nan maza da mata, tare da fatan Allah Ya karawa wannan damina albarka da yalwa.