Samar da tsaro ga sansanonin ’yan gudun hijira
Wani rahoto da Cibiyar Kula da ’Yan Gudun Hijira da kungiyar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta kasar Norway, ya nuna Najeriya ce a kan gaba wajen yawan ’yan gudun hijirar cikin gida a Nahiyar Afirka, inda ta ke da masu gudun hijira miliyan uku da dubu 300. Daga cikin wannan adadi, an raba mutum […]
Wani rahoto da Cibiyar Kula da ’Yan Gudun Hijira da kungiyar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta kasar Norway, ya nuna Najeriya ce a kan gaba wajen yawan ’yan gudun hijirar cikin gida a Nahiyar Afirka, inda ta ke da masu gudun hijira miliyan uku da dubu 300. Daga cikin wannan adadi, an raba mutum dubu 500 da muhallinsu ne a shekarar 2013 kadai, a cewar rahoton. Kuma hare-haren da ake kaiwa a yankin Arewa maso Gabas ne ya shafa da kuma wadanda wasu bala’o’i suka shafa a baya, kamar ambaliyar ruwa da rikice-rikicen kabilanci.
Samar da sauki da tsaro a sansanonin ’yan gudun hijirar zai ci gaba da kasancewa babban kalubale. Amma duk da haka yana da muhimmanci gwamnati ta sauke wadannan muhimman lalurori a sansanonin. Akwai dimbin wadanda irin wannan lamari ya shafa da ba su zaune a sansanonin ’yan gudun hijirar, akwai kuma wasu da dama a sassan kasar nan; don haka adadin wadanda lamarin ya shafa yana iya fin haka yawa. Wannan rukunin wadanda lamarin ya shafa sukan yi sauri fadawa hannun ’yan damfara. A cewar wasu daga cikinsu, musamman mata, yayin da wasu mutanen kirki ke kai kayan tallafi zuwa sansanonin, wasu matasa ko zauna-gari banza kan je su amshe kayan, inda suke hana wadanda harin ya shafa daga cin gajiyar tallafin.
Misali a sansanin ’yan gudun hijirar Gwoza da ke kauyen Kuchi Goro a Abuja wasu wakilan matasa sun ce suna fuskantar barazana daga zauna-gari banza da suke kai hari ga ayarin motocin kayan tallafin da aka tura sansanin. Mata da suke da rauni ba su iya kokawar samun kayan tallafin ta hanyar gwagwarmaya da matasan wadanda ke shirye su fafata fada a kan kayan. Rashin tsaro a irin wurare yana nufin a kullum wadannan zauna-gari banza ne za su rika sheke ayarsu.
Idan akwai wadataccen tsaro, zauna-gari banza ba za su iya shiga sansanonin ba tunda farjo, balle su rika sace kayan tallafin daga wadanda ya kamata su samu. Kuma a inda ake da matasa a cikin ’yan gudun hijirar da ke sansanonin ya wajaba a samu tsari mai kyau n araba kayan tallafin.
Wajibi ne a kan gwamnati ta tsare sansanonin, baya ga samar da kayan bukatun yau da kullum kamar ruwa da maguguna da wurin kwanciya da ya dace da kuma wuraren bahaya.
Rashin tsaro a sansanonin yana jefa mata da yara a cikin hadari fiye da maza. Kuma suna cikin hadarin haduwa da ayyukan masu fyade da sauran nau’o’in musgunawa. ’Yan gudun hijirar sun gudo ne daga wata matsala, sun bar gidaje da hanoyin samun abincinsu. Wasu sun shiga halin kaka-ni-ka-yi saboda halin da suka samu kansu. Don haka wajibi ne gwamnati ta kare su ta yadda ba za su sake fadawa a cikin wani tashin hankali ba. Wajibi ne a samu ingantaccen tantancewa a sansanonin domin a tsame wadanda ba ’yan gudun hijira ba ne da suka je can domin su rika samun na bagas daga kayan tallafin da aka tanada don ’yan gudun hijirar da aka riga aka yi musu rajista.
Ya wajaba Hukumar Bayar da Tallafin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta dauki aikin tantancewa da gano ainihin adadin mutanen da aka raba da muhallansu, maimakon dogaro da adadin da wasu kungiyoyin kasashen waje suka tattara. Rashin wannan tsari na iya zama dalilin da wasu da aka raba da muhallinsu suke zuwa suna zama da ’yan uwansu, misali a Maiduguri, suna bayyana ne kawai a lokacin karbar abinci, inda suke zuwa tare da ’yan uwansu da ba a raba su da muhallansu ba. Don haka samun adadi na gaskiya yana da muhimmanci wajen tsara al’amura da kuma dalilai na kai dauki.
Wadanda kaddara ta tilasta su zama ’yan gudun a kasarsu ta haihuwa a gaskiya akwai bukatar su kasance cikin wadanda gwamnati ta fi ba muhimmanci, bai kamata a bar su su rika fama da zauna-gari banza da sauran miyagu ba.
Wajibi ne tsaronsu da jin dadinsu ya zama abin da gwamnati ta fi kula da shi ta yadda ba wanda zai shiga cikinsu ba tare da an tantance shi ba, idan ba haka ba hatta maharan suna iya shiga cikinsu su yi da’awar su ma ’yan gudun hijira ne.
A karfafa ’yan gudun hijira su bar zama a gine-ginen marasa kyau da ba a kammala ba, a hanzarta dauke su zuwa sansanonin da aka tsara har zuwa lokacin da za a kawo karshen tashin hankalin su koma gidajensu don ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba.