Samar wa matasa aiki zai magance matsalar tsaro – Zakariya APC
Wani matashi da ke neman Jam’iyyar APC ta ba tsayar da shi takarar dan Majalisar Tarayya daga karamar Hukumar Bauchi Malam Zakariya Umar Goje, ya nuna damuwa kan Gwamnatin Tarayya ta gagara samar wa matasan Arewa aikin yi a wannan lokaci da ake ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula da ke lakume dimbin rayukan jama’a […]
Wani matashi da ke neman Jam’iyyar APC ta ba tsayar da shi takarar dan Majalisar Tarayya daga karamar Hukumar Bauchi Malam Zakariya Umar Goje, ya nuna damuwa kan Gwamnatin Tarayya ta gagara samar wa matasan Arewa aikin yi a wannan lokaci da ake ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula da ke lakume dimbin rayukan jama’a a jihohin Arewa maso Gabas. Malam Zakariya Goje ya ce lokaci ya yi da ya kamata matasa su rika fitowa takarar mukamai daban-daban domin su ne ake da tabbacin cewa da zarar sun samu mulki za su iya magance matsalar al’umma cikin kankanen lokaci. Malam Zakariya ya bayyana haka ne lokacin da wasu dimbin matasa suka kai masa ziyara domin nuna masa goyon bayan fitowa takarar dan Majalisar Tarayya a zaben 2015. Matasan sun bayyana cewa Jam’iyyar APC ce za ta iya magance matsalar ’yan Najeriya, don haka za su ci gaba da wayar da kan magoya bayan jama’a domin sun gaji da wannan gwamnati wacce ta gaza kare rayuwa da dukiyoyin al’umma.