Samar wa matasa ayyukan yi zai kawo ingantacciyar zaman lafiya -Alhaji Babayo
Wani dan kasuwa a garin Auchi na Jihar Edo, Alhaji Idirisa Babayo ya yi tsokacin da gwamnatocin kasar nan za su yarda su daukaka matakin samar wa matasa ayyukan yi, to lallai da komai zai zo da sauki kuma a samu zaman lafiya ingantacciya, wacce za ta kasance mai dorewa. dan kasuwa Alhaji Idiris ya bayyana […]

Wani dan kasuwa a garin Auchi na Jihar Edo, Alhaji Idirisa Babayo ya yi tsokacin da gwamnatocin kasar nan za su yarda su daukaka matakin samar wa matasa ayyukan yi, to lallai da komai zai zo da sauki kuma a samu zaman lafiya ingantacciya, wacce za ta kasance mai dorewa.
dan kasuwa Alhaji Idiris ya bayyana bukatar samar da hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a makon da ya gabata, inda ya nuna damuwarsa dangane da rashin kwanciyar hankalin da ake yawan samu a cikin kasa. Ya yi nunin cewa wannan wata shawara ce da yake ba gwamnatocin kasar nan, a cikin irin gudunmawar da yake ganin zai iya bayarwa don a ciyar da kasa gaba, a matsayinsa na dan kasa mai kishinta.
Ya ce duk wata kasa da take da yawan al’umma matalauta da kuma matasa, musamman irin Najeriya, amma kuma sai ya kasance gwamnatin kasar ba ruwanta da kowa, tun ma dai ba matasanta ba, kuma ba ta nuna damuwa da su, ba ta damu da ko yaya suke rayuwa ba ballantana ta samar masu da hanyoyin dogaro da kai, ba mamaki a samu kasar ta fada cikin wasu tashe-tashen hankula da za su iya lakume al’amuransu na rayuka ta yadda za a samu matsaloli mabambanta.
“A yau Najeriya ta kai matsayin da matasanmu sai yawon gararamba da barnace-barnace kawai, ba don komai ba illa kasancewar ba su da wani aikin yi, a bangaren gwamnati ko masu hannu da shuni, wadanda za su taimake su. Idan muka duba, kusan duk kamfanoni da wasu masana’antu a kasar nan gaba daya, babu mai rai, sun gama dukushewa, ta haka muka fara shiga matsaloli da suka gagare mu magance su”. Inji shi.
Sai kuma ya ce, “A hakikanin gaskiya da a ce a kasar nan muna da rayayyun masana’antu, manya da kanana, kamar yadda wasu kasashen suka rayar da nasu masana’antun, za a samu sauki. Saboda haka ina ganin, idan da gaskiya ake so, to wajibi ne mu tashi tsaye da mu da shugabanninmu, kuma masu hannu da shuni da su gwamnatocin kasa baki daya, su farfado da kamfuna da masana’antumu, wadanda da tuntuni suka dukushe tare kuma da ginin wasu sababbin, to za a kawo alheri, wanda ba a zata ba, kuma zai kawo karshen irin yawan tashe-tashen hankula da ake samu a kasar nan”.