Sambo Dasuki ya musanta fallasa wa EFCC abokan hadin bakinsa

Bayan da Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta mika tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) a ranar Talata, an rika yada labaran cewa Sambo Dasuki ya fallasa sunayen abokan hadin bakinsa.Sai Sambo Dasuki ya musanta cewa ya fallasa sunan wani ko wasu […]

Sambo Dasuki ya musanta fallasa wa EFCC abokan hadin bakinsa

Bayan da Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta mika tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) a ranar Talata, an rika yada labaran cewa Sambo Dasuki ya fallasa sunayen abokan hadin bakinsa.
Sai Sambo Dasuki ya musanta cewa ya fallasa sunan wani ko wasu kan zargin da Gwamnatin Tarayya take masa na badakalar sayo makamai na Dala biliyan biyu.
A jiya Alhamis ne EFCC ta yi wa Dasuki tambayoyi inda ta bayyana sunayen wasu fitattun ’yan Najeriya da cewa suna cikin wadanda suka amshi makudan kudi daga ofishinsa lokacin da yake Mashawarcin Shugaban kasa.
Dasuki, wanda ya yi magana ta bakin lauyansa, Ahmed Raji (SAN), ya  ce bai yi wani bayani da ya ambaci suna wani ga EFCC, sai ya ji mamakin inda masu rubuta wannan bayani suka samu labarinsu.
 “Ina tare da Dasuki jiya don haka ina fadi da babbar murya wanda nake karewa bai yi wani bayani ko ya ambaci sunan wani ko wasu ba,” kamar yadda kafar sadarwa ta PRNigeria ta ruwaito Raji (SAN) yana fadi.
 “Ku ruwaito ne a ko’ina Dasuki bai yi wani mai kama da haka ba, zuki ta malle ce kawai. Tunani ne na masu rubuta hakan don kirkiro karya bisa dalilin da suka bar wa kansu don haka ’yan Najeriya su yi watsi da haka. Suna son bata sunansa ne, su jefa shi cikin rigima ta yadda abokai da masoyansa za su kaurace masa, kuma ba za su yi nasara ba,” inji shi.
Wata majiya da ta yi magana da jaridar The Nation ce ta shaida mata cewa, Sambo Dasuki ya yi wasu bayanai ‘masu ban mamaki’ kan kwangilolin sayo makamai a ranar Talata bayan an kama shi.
Da take bayyana furucin da ya yi lokacin da EFCC take yi masa tambayoyi, majiyar ta ce: “Lokacin da aka kawo Dasuki nan, daga farko ya ki ya rubuta kowane bayani, yana zargin cewa jaridu ne suke yi masa shari’a. Ina jin tsohon Mashawarcin Shugaban kasar ya yanke shawarar ba zai yi magana ba ne bisa shawarar lauyoyinsa cewa ya bar komai sai an je kotu. Sai ma’aikatan EFCC suka ba shi kwafen bayanin da wani tsohon Daraktan Kudi a ofishin Mashawarcin Shugaban kasa, Shu’aibu Salisu inda a ciki ya yi wasu bayanai da suka fadi masu hannu a cikin badakalar.”
Majiyar ta kara da cewa: Dasuki wanda ya girgiza da ikirarin Salisu ya rika maimaita cewa: ‘Kuna nufin Salisu ne ya fadi duk wadannan? Kuna nufin shi ya fadi wadannan? Ku ba ni alkalami da takarda. Daga nan ne ya yanke shawarar yin fallasa. Ya kawo dogon jerin sunayen manyan PDP da suka amshi kudi daga ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro. Kuma ya ambaci sunan wani tsohin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa da tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci da sauransu da dama.”
Majiyar ta ce, fallasar da tsohon daraktan kudin ya yi ne ta bude kofar wannan fallasa, kuma ana ci gaba da bincike kuma EFCC za ta kama karin wadanda ake zargi nan gaba kadan.
Majiyar ta ce akwai yiwuwar EFCC ta fadada bincikenta ya hada da tsabar kudi Dala miliyan 9 da Afirka ta Kudu ta yi domin yin tambaoyi ga duk mai hannu a cikin shirin sayo makaman da bai yi nasara ba.
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa da shugaban talabijin din, Raymond Dokpesi da tsohon Minista Bashir Yuguda, wadanda ake zargi da hannu a batun sauya akalar kudin sayo makaman sun shuga hannun EFCC, sai dai suna ta kokarin cika ka’idojin belinsu, yayin da wata majiya a EFCC ta ce hukumar na shirin gabatar da wasu a gaban kotu don ba ta damar yi wa mutum 22 da ake zargi tambayoyi a yayin da suke hannunta, hukumar tana tunanin manyan masu hannu a lamarin suna iya garzayawa kotu don neman a kare musu mutuncinsu na dan Adam wanda hakan zai iya kawo cikas ga bincikenta.
A bangaren shugaban talabijin din AIT, Dokpesi, ya ce Naira biliyan biyu da miliyan 100 da ya karba daga ofishin mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro a zamanin mulkin Jonathan na biyan kafafen watsa labarai da kamfe din siyasa kan zaben bana.
Dokpesi wanda EFCC ta tuhuma a ranar Talata kan wannan adadin kudi da ya karba, a wata sanarwa da kamfaninsa ya fitar a shekaranjiya Laraba ta bayyana cewa Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ne ya gayyace shi don “Ya yi karin bayani kan wasu kudade da aka biya shi daga ofishin tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro, Malam Sambo Dasuki. Kuma Dokpesi ya bayyana wa jami’an EFCC cewa Naira biliyan 2.1 da ya karba daga ofishin kudin tallace-tallace da kamfe ne a kafafen watsa labarai lokacin zaben shekarar 2015,” kamar yadda wata majiya ta ruwaito kamfanin yana fadi.
Wani daga cikin wadanda EFCC ta kama mai suna Abba M.T. Usman, ana zargin an biya shi kudi ya sayo helikwaftoci shida da wasu harsasai, amma bai sayo ko daya ba. Ana zargin Raymond Dokpesi da karbar Naira biliyan 2.1m sai tsohon Minista Bashir Yuguda Naira biliyan 3, sai Bafarawa Naira biliyan 4.6 daga asusun Babban Bankin Najeriya kan Yaki da Boko Haram.

Mukarraban Dasuki da aka kam sun hada da:
1)     Shu’aibu Salisu, Daraktan Kudi a ofishin Dasuki kuma ma’aikacin Hukumar Leken Asiri ta kasa (NIA),
2)     Aminu Baba Kusa, tsohon Babban Daraktan Kamfanin Man fetur na kasa (NNPC),
3)     Mohammed Baba-Kusa dan Aminu Baba Kusa
4)     Abba M.T. Usman,
5)     Ebegny Kundaeb,
6)     Attahiru Maccido,
7)     Salisa Umar Garu,
8)     Oyinmiebl Bribena,
9)     Olukoya Olusegun Godwin,
10)     Olukayode Raimi.
11)     Bashir Yugudu
12)     Alhaji Attahiru Bafarawa
13)     Sagir Attahiru Bafarawa
14)     Abba Bello Halliru
15)     Shu’aibu Salisu.