Samfurin noman ranin Green House na Fadama III ya kankama a Filato

Shirin noman rani na zamani, na Green House da Fadama III suka fara gudanarwa a Jihar Filato ya kankama. Shi dai wannan sabon tsari na noman rani na Green House, da ake gina babban dakin leda a rufe, ayi kunyakai a ciki, a haka rijiyar burtsatse tare da samar da tankin ajiye ruwa, da  robobin […]

Samfurin noman ranin Green House na Fadama III ya kankama a Filato

Shirin noman rani na zamani, na Green House da Fadama III suka fara gudanarwa a Jihar Filato ya kankama. Shi dai wannan sabon tsari na noman rani na Green House, da ake gina babban dakin leda a rufe, ayi kunyakai a ciki, a haka rijiyar burtsatse tare da samar da tankin ajiye ruwa, da  robobin da ake tura ruwa zuwa cikin gonar. Fadama III ne suke yi wa kungiyoyin matan da mazajensu suka rasu, da mata  ma’aikata da suka yi ritaya da kuma matasa kyauta a jihar ta Filato.

Binciken da wakilinmu ya gudanar dangane da wannan shirin noman rani na Green House a jihar ta Filato, ya gano cewa ya zuwa yanzu, Fadama III sun ginawa kungiyoyin mata da matasa irin wadannan dakuna na wannan tsarin noman rani, guda 10 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Bassa da Barikin Ladi da kuma Mangu.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci daya daga cikin irin wadannan gonaki a kauyen Rantiya da ke karamar hukumar Jos ta Kudu, ya iske matan da aka ginawa wannan gona suna ta gudanar aiki a cikin gonar.

Da take zantawa da wakilinmu, daya daga cikin matan, Misis Esther Bitrus ta bayyana cewa kungiyarsu da ta kunshi mata 12, da suka hada da matan da mazajensu suka mutu da kuma matan da suka yi ritaya ne suka sami shiga wannan shiri.   

Ta ce ya zuwa yanzu ana nan ana koya masu yadda za su yi wannan noma, na Green House. Ta ce wannan noman lambu da ake koya masu ya yi daban da irin wanda suke yi ada. “Babu shakka wannan noma zai taimaka mana domin akwai alheri a ciki. Don haka muna kira ga mata su hada kai su shiga wannan shiri na noman rani na Green House. Haka kuma muna godiya ga shugaban Fadama III na Jihar Filato kan taimakawar da ya yi mana”.

Wakilinmu ya tuntubi shugaban Famada III na Jihar Filato, Mista Gideon Dandam kan manufar kirkiro wannan shirin  noman rani na Green House da abin da ya kunsa. Mista Gideon Dandam ya yi bayanin cewa ana noman tumatur lokacin rani da damina amma babban abin da yake damun tumatur, shi ne matsalar fara. Kuma tumatur yana bukatar ruwa a lokacin rani.

Ya ce don haka suka ga cewa ya da ce su bi wata hanya da zata taimaka wajen rage matsalar fara da take cin tumatur da kuma magance matsalar ruwa. Don haka suka kawo wannan noman zamani na Green House.

Ya ce wannan tsarin noman wani tsari ne da ake rufe gonar da aka yi da leda, ayi kamar gini, wanda ba zai hana rana shiga ba. Kuma akwai wasu robobin tura ruwa da ake sanyawa kan kunyakin da aka yi, kuma akwai kofa a kowane gindin shuka, wanda ruwa yake sauka a jikin shukar kadan kadan.  

Har’ila yau ya ce amfanin gonar da za a samu a wajen wadannan kunyakai, zai ninka amfanin da za a samu, a eka biyar na wanda aka yi a waje. Ya ce wannan tumatur yana yado ne a sama kuma za a iya yin watanni shida ana dibarsa, kuma tushe daya na wannan tumatur zai iya bada ‘ya’ya masu nauyin kilo 100.

“Irin wannan tumatur ana gwada nauyinsa ne wajen sayarwa, ba a kwando ake zuba shi ba. Kuma kilo daya na wannan tumatur yana kai wa naira dari shida. Kuma wanda ya noma irin wannan tumatur ba shi da wata matsala, wajen sayarwa domin ana zuwa ne a ajiye kudi a wajen wanda yake noma irin wannan tumatur”.

Sannan sai ya yi kira ga manoma da su hada kai su rungumi wannan noma na Green House domin wannan noma ba shi da wata wahala, sai dai mutum ya bude fanfon ruwa ya tafi zuwa kunyakan gonar. 

Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, wani babban jami’i da ke kula da wannan shiri na Green House a jihar ta  Filato, Mista James Dachomo ya bayyana cewa Famada III suna yi wa nakasassu da matan da mazajensu suka mutu da mata ma’aikata da suka yi ritaya kuma da matasa ne. Ya ce wadanda suka sami shiga wannan shiri ba a karbar ko kwabo daga wajensu.

“Wannan noma kamar wata makaranta ce aka samarwa manoma, don haka muna kira ga wadanda suka amfana su daraja wannan shiri da kyau, domin an yi ne don taimaka masu da iyalansu. Kuma su yi amfani da wannan dama su kara yin wasu dakanun, domin wannan rijiyar burtsatse da aka yi masu zai iya daukar wajen irin wannan gini kamar guda 10”.