Saminu Isa ne zakaran gasar karatun Alkur’ani na bana a Legas
dalibin makarantar Islamiyya ta Nurul Yakeen da na makarantar Ta’alimul Arabiyya su ne suka zama zakaru a gasar karatun Alkur’ani da cibiyar binciken al’amuran addinin Musulunci (Islamic Research Center) da ke Legas ta shirya.daliban da suka yi nasara sun hada da Saminu Isa daga makarantar Islamiyya ta Nurul Yakeen, wanda ya yi nasara a bangaren […]
dalibin makarantar Islamiyya ta Nurul Yakeen da na makarantar Ta’alimul Arabiyya su ne suka zama zakaru a gasar karatun Alkur’ani da cibiyar binciken al’amuran addinin Musulunci (Islamic Research Center) da ke Legas ta shirya.
daliban da suka yi nasara sun hada da Saminu Isa daga makarantar Islamiyya ta Nurul Yakeen, wanda ya yi nasara a bangaren Izifi biyar da maki 92, sai Fadimatu Abubakar Kalla daga makarantar Ta’alimul Arabiyya da ta yi nasara a bangaren Izifi biyu da maki 90.
Sai Ibrahim Sani Tofa, wanda ya wakilci makarantar Faidiyya a izifi biyar, inda ya zo na biyu da maki 84. Shi kuwa Abubakar Muhammad daga makarantar Ta’alimul Arabiyya ya zo na uku da maki 63.
Sauran sun hada da Hauwa Umar, wacce ta wakilci makarantar Al Faidiyya da ta zo ta biyu da maki 89, sai Khadija Sani daga makarantar Darul kur’anil Kareem da ta zo ta uku da maki 63.
Majidadin Agege, Alhaji Aliyu Abubakar ya baiwa daliban da suka yi nasara kyautar kwamfuta, sannan kuma ya baiwa matan da suka yi nasara kyautar Naira dubu uku kowaccensu.
Haka zalika dalibin da ya zo na daya ya samu kyautar janareto; na biyu da na uku kuwa sun sami kyautar fankoki. Sannan an ba wa sauran makarantun da suka shiga gasar kyaututtuka daban-daban.
Da yake bayani, shugaban cibiyar, Ustaz Aminu Dauda ya ce sun shirya gasar ne don zaburar da daliban makarantu wajen haddar Alkur’ani.
Ustaza Aminu ya ce, “Tun lokacin azumi muka fara gasar kuma dalilin da ya sa muka shirya ta a lokacin azumi shi ne saboda lokacin hutu ne na makarantu, a maimakon a bar yara su zauna haka ba sa komai, sai muka ga ya dace mu shirya gasar don mu zaburar da su wajen haddar Alkur’ani kuma burinmu shi ne gasar ta samu karbuwa ba a Jihar Legas ba kowai, har da kasa baki daya”.