Samun fata mai sheki

Shin fatarki na da gautsi ko laushi? Fatarki tana da taushi, sheki ko babu? A yau mun kawo miki wani tsari da za ki yi amfani da shi don samun fata mai sheki da kuma laushi. Ya kamata ki kula da fatarki kasancewar fata na kara wa mace kyau.Gulli ko gurji (cucumber) na taimakawa wajen […]

Samun fata mai sheki
Samun fata mai sheki

Shin fatarki na da gautsi ko laushi? Fatarki tana da taushi, sheki ko babu? A yau mun kawo miki wani tsari da za ki yi amfani da shi don samun fata mai sheki da kuma laushi. Ya kamata ki kula da fatarki kasancewar fata na kara wa mace kyau.
Gulli ko gurji (cucumber) na taimakawa wajen sanya fata ta yi sheki. Gulli ko gurji na kama da kankana, kashi 95 dinsa ruwa ne. Kuma yana dauke da sinadarin bitamin C. Gulli ko gurji  na daga cikin ‘ya’yan itacen da ya kamata mace ta rika ci domin ta samu lafiyar jiki. Yana wanke maikon da ke cikin jiki. Idan kina son rage kiba to ki rika cin sa

Ga yadda za ki hada:
·         Ki dauki gurji ko gulli daya, ki bare, sannan ki yanka shi gunduwa-gunduwa, kananan yanka.
·         Ki markada gulli ko gurji a na’urar bilendarki, sai ki tace ruwan a kofi.
·         Bayan haka, sai ki zuba ruwan a kwalba, sai ki zuba cokali 2 na zuma a ciki.
·         Kafin ki yi amfani da wannan hadin, ki girgiza kwalbar sosai don ruwan gurji da zumar su gaurayu sosai.
·         Ki zuba hadin kadan a kan auduga, sai ki shafa a fuskarki, zuwa wuya da kuma sauran jikinki na tsawon minti 3 zuwa 4. Ki rika shafa wannan hadin sau biyu a rana; da safe da kuma yamma. Za ki iya amfani da sauran hadin na tsawon sati daya kafin ki sake hada wani idan kina sanya shi a firij.