Samun hadin kan tsofaffin shugabanni zai taimaka wa yaki da rashawa – Al-Ilory

Tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kwara, Muhammad Amir Abdulkadir Al-Ilory na PDP a shekarar 2011, ya bayyana cewa, muddin Shugaba Buhari ya na son cimma nasara kan yakin da rashawa a kasar nan, to sai ya hada kai da tsofaffin shugabannin kasar, domin a cewarsa duk da ana zarginsu da hannu game da halin da […]

Samun hadin kan tsofaffin shugabanni zai taimaka wa yaki da rashawa – Al-Ilory

Tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kwara, Muhammad Amir Abdulkadir Al-Ilory na PDP a shekarar 2011, ya bayyana cewa, muddin Shugaba Buhari ya na son cimma nasara kan yakin da rashawa a kasar nan, to sai ya hada kai da tsofaffin shugabannin kasar, domin a cewarsa duk da ana zarginsu da hannu game da halin da kasar na ta shiga, amma a yanzu suna da burin bar wa kasar nan gadon abin arziki.

Al-Ilory, ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kawo Kamfanin  buga jaridun Daily Trust da Aminiya a farkon wannan makon, inda ya tabo batutuwa da dama kan al’amuran kasar nan, musamman ma a wannan lokaci da shugaba Muhammadu Buhari ke jinya a Landan. “Ba na jin irin su Cif Obasanjo da Ibrahim Babangida su na da burin kwasar dukiyar kasar nan a yanzu. Kuma babban burinsu tabbas bai wuce su bar wa kasar nan gadon abin arziki ba, wanda zai zamo abin koyi ga ’yan baya. 

Sannan kuma ya ce sukurkucewar tsaro na da alaka da tafiyar Shugaba Buhari jinya, “Harkokin tsaro sun sake tabarbarewa, har takai ga ana samun karuwar yunkurin hare-haren Boko Haram da garkuwa da mutane. Duk da cewa Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yana iya kokarinsa, amma kima da mutuntakar shugaba Buhari da aka zaba tana taimakawa wajen rage wasu al’amuran.” 

Da aka tambaye kan yadda ’yan siyasa suka sauya sheka daga PDP zuwa APC, amma har yanzu yana PDP, sai ya ce: “A shekarar 2007 na jagoranci tawagar yakin neman zaben Marigayi Shugaba ’Yar’Adua, da ya ci zabe bai ba ni mukami ba, amma ya ba ni mai bayar da shawara na sirri. Kuma na yi masa aiki gwargwadomn hali. Don haka abin da nike so jama’a su fahimta shi ne, ni kasar ce a gabana ba jam’iyya ba, shi ya sa ko wane ne ke mulki in na samu dama zan ba shi shawarar da ta dace.”

Da yake Karin haske kan manufarsa ta tsayawa takarar gwamna a Jihar Kwara ya ce ko yanzu in mutanensa suka nuna bukatar ya zo ya yi musu hidima tabbas a shirye yake, domin yana da fahimtar cewa jihar kwara za ta iya rike kanta da noma kawai in an yi tsari mai kyau da zai taimaka wa manoma. Game da manoman Zimbabuwe da tsohon Gwamnan Jihar ya gayyato, Sanata Bukola Saraki, cewa ya yi, da farko mutanen Jihar Kwara sun matukar farin ciki, domin yadda aka nuna musu cewa hadin gwiwa za su yi da manoman Zimbabuwen, amma daga bisani sai suka ga lamarin ya sha bamban.

“An nuna wa mutanenmu cewa za su hadu da bakin manoman ayi noma, amma sai suka ga wani tsari daban, inda aka kwace gonakinsu, aka bai wa fararen fatar, sannan ake so su zo su yi wa bakin bauta. Don haka dai har yanzu babu wanda zai ce maka ga irin tsari ko yarjejeniyar da aka kulla da su, sai dai tsohon Gwamna Sanata Bukola Sarki da gwamnan jihar na yanzu.”

Ya yi bayani game da kafa kananan matatun fetur, kamar yadda ake a kasar Malesiya da sauran kasashen Asiya, wato ‘Modular refinery.’ 

A cewarsa: “Idan aka kafa irin wadannan kananan matatun za a shawo kan matsalar man fetur a Najeriya,” a cewarsa.