Samun kadaitaccen tunani yana taimakon rayuwa
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum. Haka kuma zan ba ku hakuri saboda rashin ji na na tsawon wata daya cur. Wannan ya faru ne sakamakon tafiya hutun shekara da na yi. Na yi kwauron bakin sanar da ku kafin in tafi, don haka a yi […]
Ya ku ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum. Haka kuma zan ba ku hakuri saboda rashin ji na na tsawon wata daya cur. Wannan ya faru ne sakamakon tafiya hutun shekara da na yi. Na yi kwauron bakin sanar da ku kafin in tafi, don haka a yi mani afuwa kan haka. A wannan makon da ikon Allah za mu ci gaba da ganawa da juna cikin tambihin zizara wa rayuwarmu sinadaran kyautata mana rayuwa. Allah sa mu dace, amin.
A wannan karon za mu duba sabon maudu’i ne kamar yadda muka nuna a sama. Hakika akwai gaskiya a batun cewa mutum ya rika samun kadaitaccen tunani, hakan zai taimaka masa a rayuwa. Ma’anar haka ita ce, yana da kyau mutum a cikin rayuwarsa ya rika samun lokaci na musamman yana kadaicewa, sannan ya dukufa cikin tunani mai zurfi.
Rayuwar dan Adam tana cike da kalubale, tana dauke da yanaye-yanaye masu bambanci da juna. A tsawon rayuwar mutum, yakan shiga lokacin da yake samun farin ciki, kamar kuma yadda wani lokacin yake samun bakin ciki da bacin rai. Wasu lokutan mutum kan samu nasara a harkokinsa, kamar yadda kuma wasu lokutan yake samun akasin haka.
Duka dai a rayuwar dan Adam, mutum kan kasance cikin zumunci da aminci da lumana da abokan zamansa ko makwabtansa ko ’yan uwansa. Haka kuma a wani janibin, mutum kan kasance cikin sabani, rigima ko hairani da abokansa ko ’yan uwansa ma na jini.
dan Adam yana da wata irin halitta, wacce Allah cikin ikonSa Ya samar masa. Mutum halitta ne mai rauni kwarai da gaske, domin an halitta shi ne a matsayin mai kasawa, wanda zai iya yin kuskure a wasu lokuta, wasu lokutan kuma zai iya aikata daidai.
Zuciya da kwakwalwar mutum suna taka muhimmiyar rawa a jikin dan Adam. Wadannan halittu biyu, su ne ginshikai kuma su ne linzaman da ke jagorancin tunani da ayyukan dan Adam. Kamar yadda masana suka fada, kwakwalwa ce ke hasko wani al’amari, nan take kuma sai ta aika shi zuwa zuciya. A zuciyar ne ake nikawa da markadawa da tace wannan tunani, kafin daga bisani a mayar da shi zuwa kwakwalwa, wacce za ta ba gangar jiki umarni don ya aiwatar da dukkan abin da aka umurce shi.
Mun yin wannan shara da tariya ne duk domin mu warware jigonmu na yau – samun kadaitaccen tunani yana taimaka wa rayuwa. Wannan na faruwa ne saboda rayuwar gaba dayanta tana tafiya ne bisa gwadabe biyu, hanya mai kyau da marar kyau, hanyar hankali da wacce ta saba wa hankali, hanyar daidai da kuma karkatatta.
A duk lokacin da ka ga mutum ya aikata wani abu da aka yi ittifakin cewa aikin kwarai ne, to babu shakka ya samu dace da haka ne sakamakon kyakkyawan tunanin da ya fito daga kyakkyawar zuciyarsa. Haka ma idan mutum ya aikata akasin mai kyau, duk dai hakan na faruwa ne a sakamakon gurbataccen tunani.
An samu bayani daga Fiyayyen Halitta, Manzon Allah (SAW) cewa a jikin dan Adam akwai wata tsoka, idan ta gyaru, to dukkan gangar jiki ta gyaru. Wannan ke kara tabbatar mana da cewa, duk zuciyar da ta samu tarbiyyar tunani mai kyau, duk zuciyar da ta ladabtu da ingantacce kuma tataccen tunani, babu abin da zai fito daga gare ta sai aiki mai kyau. A daya bangaren kuma, zuciyar da aka bari ta susuce da gurbataccen tunani, babu abin da za ta rika samarwa sai gurbataccen tunani, babu abin da gabobin jikin da ke dauke da ita zai aiwatar sai gurbataccen aiki; aikin Allah-wadai, wanda ba zai tsinana wa al’umma komai ba.
Ina ganin ko nan na tsaya, za mu gane inda maudu’inmu na yau ya fuskanta. Amma dai bari mu ci gaba domin kakare manufarmu. Har yanzu dai muna cewa, samun kadaitaccen tunani yana taimakon rayuwa. To wadanne hanyoyi ya kamata mu bi domin mu samu irin wannan kadaitaccen tunani?
Domin dacewa da irin wannan tunani, ya kamata mutum ya rika ware wani kebantaccen lokaci na musamman, misali sau daya a mako; ya rika kebancewa a wurin da babu sauti ko hayaniyar kowa. Mutum idan ya kebe, ya shagaltu da tunanin dukkan al’amuran da ya aikata a tsawon makon da ya gabata. Idan da hali, ya ci gaba da tunanin dukkan abubuwan da suka faru a tsawon watan da ya gabata. Idan ma yana da lokaci, ya ci gaba da tunanin, ya hasko irin muhimman abubuwan da suka faru da shi a tsawon shekara guda da ta gabata a rayuwarsa.
Sakamako: Matukar mutum ya samu irin wannan yanayi, babu shakka tunaninsa zai hasko masa kyawawa da munanan abubuwan da suka faru a lokacinsa na baya. Zai gano ayyukan kirki da ya aikata, kamar kuma yadda zai hasko ayyukan banza da gurbataccen tunaninsa ya ingiza shi ya aikata. Wannan abu shi ake kira hisabi.
Amfanin irin wannan kebantaccen tunani ga mutum shi ne, zai amfana da samun natsuwa nan take. Mutum zai gane kura-kuran da ya aikata a rayuwarsa ta baya, sannan zai iya kintsa tunaninsa domin kauce musu. Irin wannnan kebantaccen tunani zai taimaki mutum ya gano ayyukan kwarai da ya aikata, wadanda kuma tunaninsu za su faranta masa rai a nan take, sannan zai kara daura niyya da kudurta ci gaba da aikata su a rayuwarsa ta gaba.
Maudu’inmu – Samun kadaitaccen tunani yana taimakon rayuwa. Mu jaraba mu gani, ’yan uwa!