Sanƙarau ta kashe ɗalibai 20 a Yobe
A gaskiya dai ba zan iya bayar da haƙiƙanin adadin ɗaliban da abun ya shafa ba saboda akwai waɗanda aka kwantar a asibiti.
Ana fargabar cewa sanƙarau ta yi sanadiyyar mutuwar ɗalibai 20 a wasu makarantu uku na kwana da ke kananan hukumomin Potiskum, Fika da Fune a Jihar Yobe.
Bayanai sun ce cikin makarantun na gwamnati da barkewar annobar ta sanƙarau ta shafa sun haɗa da biyu na mata sai kuma guda ta maza.
- Sanatoci sun tabbatar da naɗin Shugabar Hukumar NFIU Hafsat Bakari
- ’Yan takara sun bijire wa taron da Shugaba Macky Sall ya kira
Wata majiya a garin Potiskum ta shaida wa Aminiya cewa, mutuwar ɗaliban 20 na zuwa ne bayan an kwantar da su a babban Asibitin Potiskum inda suke samun kulawa.
Kwamishinan Ilimi a Matakin Farko da Makarantun Sakandire, Dokta Muhammad Sani Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, akalla ɗalibai 20 ne suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wata cuta da ake zargi sanƙarau ce.
Kwamishinan ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin cewa a gaggauta ɗaukar duk wani mataki da ya dace domin yi wa tufkar hanci dangane da barkewar cutar.
Ya ƙara da cewa, a halin yanzu akwai ɗalibai da dama da ke kwance a Asibitin na Potiskum waɗanda suka nuna alamun kamuwa da cutar ta sanƙarau.
“Wannan cuta ce daga Allah kuma babu wanda zai iya tsere mata muddin ta zo. Sai dai dole mu tashi tsaye domin dakile yaduwarta zuwa sauran wurare.
“Daga cikin matakan da muka ɗauka shi ne sanya malamai uku-uku duk bayan awa uku su riƙa rangadin kula da koshin lafiyar ɗalibai a makarantun da lamarin ya shafa.
“Mun kuma tanadi motocin bayar da agajin gaggawa a dukkanin makarantun.
“A gaskiya dai ba zan iya bayar da haƙiƙanin adadin ɗaliban da abun ya shafa ba saboda akwai waɗanda ke karɓar magani a cibiyar killace waɗanda ake zargin sun kamu da cutar baya ga waɗanda ke kwance a asibiti suna karɓar magani,” a cewar Kwamishinan.