Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi
Alamomin cutar sun haɗa da sanƙarewar wuya, zazzaɓi mai zafi, rashin son haske, ruɗewa, ciwon kai da amai.

Gwamnan Kebb Nasiru Idris
Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi.
Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa uku daga ciki kalau suke.
A cewar kwamishinan, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, da Jega, inda aka samu asarar rayuka 15 a Gwandu, shida a Jega, huɗu a Aleiro, ɗaya kuma a Argungu.
Ya ce an buɗe sansanonin keɓe waɗanda suka kamu, yayin da gwamnatin jihar ta soma ɗaukar matakan daƙile cutar ciki har da neman alluran rigakafin.
Kwamishinan ya gargaɗi jama’a game da shan magunguna da kansu, inda ya ce mutane su gaggauta zuwa asibiti mafi kusa domin yin gwaji a duk lokacin da ba su da lafiya don tabbatar da halin da suke ciki.
“Ya kamata mutane su guji yin barci a cikin ɗaki mai cunkoso. Su riƙa wanke hannayensu akai-akai bayan sun shiga bayan gida.
“Ya kamata su daina ziyartar sansanonin da aka keɓe marasa lafiyar kuma su tabbatar sun wanke ’ya’yan itatuwa da sauran kayan abinci kafin su ci don guje wa kamuwa da cutar Sanƙarau,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir Idris ya bayar da naira miliyan 30 domin siyan magunguna da sauran kayayyaki domin ɗaukar matakan daƙile cutar.
Sanƙarau wata cuta dai da ke janyo kumburi a wani rukuni na ƙwaƙwalwa ta kuma karya garkuwar ƙashin baya.
Alamomin cutar sun haɗa da sanƙarewar wuya, zazzaɓi mai zafi, rashin son haske, ruɗewa, ciwon kai da amai.
A bayan nan ne hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu.
Cikin jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa har da Kebbi.