Sana’a ta hana ni dogaro da wadansu – Kauna Yakubu
Aminiya: Kin yi karatun aikin jarida ne, amma kina sana’ar Takalma da Jakukkuna na mata, me yasa kika zabi ki zama mai sana’a ba ma’aikaciya ba? Kamar yadda na gaya maka tun farko sunana kauna Yakubu Mela, na yi Difloma ne a bangaren aikin jarida a wata kwaleji da ke garin Jos. Na kuma yi […]
Aminiya: Kin yi karatun aikin jarida ne, amma kina sana’ar Takalma da Jakukkuna na mata, me yasa kika zabi ki zama mai sana’a ba ma’aikaciya ba?
Kamar yadda na gaya maka tun farko sunana kauna Yakubu Mela, na yi Difloma ne a bangaren aikin jarida a wata kwaleji da ke garin Jos. Na kuma yi abin da ake kira IT wato sanin makamar aiki da gidan jaridar Nigeria Standard. Da na gama sai na tafi garin Kano na koyi yadda ake
yin Takalmi da Jaka da sarkoki na mata domin tun tashi na na fi sha’awar na yi sana’a na dogara da kaina ba da abin hannun samari ko na ‘yan uwa ba. Shi ya sa na ki yin aikin jarida na kama sana’a.
Aminiya: Tun kamar yaushe kika fara wannan sana’a ta yin jaka da Takalma?
Na fara ne tun shekarar 2012 lokacin da na gama karatu, sai na je Kano musamman don in koyi wannan sana’a, kuma Alhamdulillahi yanzu ita na iya kuma ita nake yi da ita kuma na dogara.
Aminiya: A lokaci daya ne kika koyi yin jaka da takalmin ko a lokaci daban daban ne?
Ba a lokaci daya na koya duka ba sai dai a waje daya ne domin wanda ya koya min yin Takalmi a wajen sa na koyi Jaka ba tare da yasan na iya ba. Dalili shi ne, shi Takalmi yake koya min da yake yana yi duka, ni kuwa a hankali ina kallon yadda yake yi sai wata rana dana koma gida na je na sayi kayan yin jaka na yi na kawo masa ya gani sai ya tambaye ni waye ya yi sai na ce masa ni ce, shi ne ya yi mamakin yadda aka yi ba tare da ya nuna min yadda aka yi ba na koya. Shi ne ya ce lailai ina da saurin koyon abu domin duk matan da suke koyan aiki a wajen babu wacce ta yi sauri koyan aiki kamar ni.
Aminiya: Tsawon wane lokaci kika dauka kafin ki iya wannan sana’a?
A gaskiya ban dade ba, don duka-duka ban wuce mako uku zuwa wata daya ba. Bayan nan sai na ci gaba da zama a wajen ina kara kwarewa, nima kuma a Unguwa idan na dawo ina koya wa wadansu.
Aminiya: Yanzu da kika zama mai cin gashin kanki da jarin nawa kika fara?
Na fara ne tun ba ni da jari, idan na samu dubu 1 ko dubu 2 sai in sayi kayan aiki ina Tarawa. Idan suka taru sai in hada takalmi da jaka ina ajiyewa. Da na tara Takalma kafa 40 Jaka seti 10 sai na sayar, shi ne sai na samu kudin da suka kai naira dubu 40 sai na dauki dubu 30 na sayi kayan aiki ina ci gaba har zuwa yanzu da na mallaki jari mai tsoka kuma a cikin gidanmu nake yi, amma nan gaba zan nemi waje babban na musamman.
Aminiya: Takalman kala daya kike yi ko kala daban-daban ne?
Eh kala daban daban ne kuma kudin ma ya bambanta, domin akwai wadanda nake musu ado da bit, kudinsu daban da wanda ban sa musu bit ba domin bit din yana karawa takalman kwalliya ne.
Aminiya: A matsayinki na mai sana’ar hannu ya kalubalen wannan sana’ar take?
kalubalen shi ne yanzu tattalin arziki ya shiga garari a kasar nan kowa yana ji a jikinsa sannan kuma wani lokaci idan na kai kayan dana hada kasuwa wajen, sai ka ji suna cewa da ba wannan kalar na yi ba da kala kaza ne don zai fi shiga. Ka ga anan idan ba a sayi wadannan ba sai su kusan zama maka asara, ga kuma wani lokacin kayan aiki ba na samun mara kyau.
Aminiya: Ya rufin asirin wannan sana’a take?
Sana’a akwai rufin asiri sosai domin ta sa na zama mai dogaro da kaina, har ina taimaka wa wasu. Sannan kuma ba na tsayawa tambayar samari kudi ko wani dan uwana, don babu abin da bana yi wa kaina a dalilin wannan sana’ar, tun daga kan sabulun wanka da sutura da bukatu na yau da kullum.
Aminiya: Mutane nawa kika koyawa wannan sana’a a yanzu wadanda suma za su yi alfahari da ita?
A nan Gombe ban koyawa kowa ba tukuna saboda jama’a da yawa suna ganin yadda nake yi suna cewa sana’ar maza ce, wai ya za ayi mace ta shiga. Amma yanzu haka wasu mata da samari sun zo sun same ni sun nuna sha’awar in koya musu, kuma na basu lokaci zuwa nan gaba kadan kafin na kammala wani shiri da nake yi.
Aminiya: Kin taba samun tallafi daga gwamnati ko wasu jama’a?
Ban samu tallafi daga wajen kowa ba, amma idan na samu zan so don bunkasa wannan sana’a ta zama kamfani da jama’a da yawa za su zo su koyi aiki, sannan a samu saukin tashi daga jihohin Arewa maso Gabas zuwa Kano don sayen kayan aiki ko sarin Takalma da jaka irin wadannan.