Sana’ar askin zamani ta yi min komai —Bala Mai Aski
‘Babu abin da ban mallaka ba daga gidan kaina da iyali da abin hawa ga kuma shagon sana’ar.’
Wani matashi mai sana’ar aski irin na zamani Malam Bala Mai Aski da ke zaune a Unguwar Matsango a garin Azare a Jihar Bauchi ya ce sana’ar aski ta inganta rayuwarsa har yana tallafa wa wadansu.
Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya kamar haka:
Kafin ka fara wannan sana’a ta aski me kake yi?
Gaskiya kafin in fara wannan sana’a ta aski bayan na dawo daga almajiranci na fara sana’ar acaba ce wato haya da babur, inda na dauki tsawon lokaci ina yin acaba.
To, ina cikin hakan ne sai babur din da nake aiki da shi ya lalace saboda hadarin da na yi da shi.
Ina zaune ba aiki, shi ne sai wani mai aski mai suna Malam Salisu da a dalilin daukar shi da nake yi a acaba ya ga na dade ba na aiki shi ne ya tambaye ni abin da ya faru, na gaya mishi yadda lamarin ya kasance.
Sai ya ce min ai gara in nemi wata sana’ar maimakon zama haka, inda ya yi min tayin in je ya koya min aski. Nan take sai na je shagonsa na fara koyon sana’ar aski da a yau nake alfahari da ita.
Na shafe kusan shekara hudu ina koyo, tun daga shekarar 2003 zuwa 2007 inda ya yaye ni na zama mai cin gashin kaina.
Bayan yaye ka yaya aka yi ka kama shagon aski?
Kanina ne ya fara biya min kudin shagon da na kama, daga nan kuma abokaina ma sun taimaka, inda suka saya min akasarin kayayyakin askin wanda a yanzu haka har na samu damar tsayawa da kafafuna, na kuma kai ga daukar yara irin su Idrisa Malam Baffa da sauransu na kuma yaye su tuntuni.
A zancen da nake yi a yanzu, na yaye yara shida wadanda suke da shagunan kansu tare da yaran da suke koya musu wannan sana’a ta aski.
Wane ci gaba ka samu daga fara wannan sana’a taka?
Alal hakika na samu ci gaba mai yawa a wannan sana’a, wadda zan iya cewa ta yi mini komai a rayuwa.
Domin kuwa kusan zan ce babu abin da ban mallaka ba tun daga gidan kaina da iyali da abin hawa ga kuma shagon gudanar da sana’ar, abin sai in ce tabarakallah!
Ko kana da wani kudiri don sake bunkasa sana’ar taka ta wajen sake bude wasu rassa?
Kwarai kuwa, ai zancen da ake yi a yanzu haka ma na bude sabon shagon gudanar da wannan sana’a tawa ta aski a Kano a wani wuri da ake ce da shi Dorawar Na’abba, kuma alhamdulillah na fara ganin falalar hakan.
A karshe wane kira kake da shi ga masu sana’a irin taka da sauran sana’o’i?
Haka ne, ina kira ga al’umma su dage don ganin sun taimaka wa matasanmu don a rage zaman kashe wando a tsakanin matasa.