Sana’ar aya tana samun tagomashi a Kalaba – Ishaka Mai Aya

Sana’ar sayar da aya a Kurmi tana samun tagomashi, musamman, yan asalin Kurosriba suna saye, suna sarrafa ta zuwa kunun aya da sauran abubuwa daban-daban. Ishaka Mu’azu na daya daga cikin masu sana’ar sayar da aya Kalaba, Jihar Kurosriba. A tattaunawarsa da Aminiya ya yi bayanin yadda sana’ar ke gudana da sauransu:   Tun yaushe […]

Sana’ar aya tana samun tagomashi a Kalaba – Ishaka Mai Aya

Sana’ar sayar da aya a Kurmi tana samun tagomashi, musamman, yan asalin Kurosriba suna saye, suna sarrafa ta zuwa kunun aya da sauran abubuwa daban-daban. Ishaka Mu’azu na daya daga cikin masu sana’ar sayar da aya Kalaba, Jihar Kurosriba. A tattaunawarsa da Aminiya ya yi bayanin yadda sana’ar ke gudana da sauransu:

 

Tun yaushe ka fara sana’ar sayar da aya?

Na samu shekara 30 ina sayar da aya, na kuma fara wannan sana’a ce tun a Tudun Wadar dankadai; tun lokacin mulkin Janar Babangida.

Aya suna ta tara, ko nau’uka nawa ke akwai nata?

Aya ta kai nau’i uku, akwai ta ruwa, akwai kanana kuma akwai manya. 

  Aya ta ruwa ita ce wadda ake sanyawa a ruwa, a jika, a wanke ta, a fitar da dusarta sannan a sayar wa masu saye suna ci, domin sha’awa ko wata bukata.

Shin ko ana iya sarrafa aya zuwa nau’in abinci ko na sha?

Eh, ana yin kunu da ita manyan, kananan ma ana yi da ita, ana yin madara da ita. Ban da wadannan ma, har biskit ana yi da ita. In sha Allahu muna sa rai gaba ma za a iya sarrafa ta zuwa wani nau’in abincin.

To, yaya cinikin, yana ja kuwa a nan Kalaba, ganin cewa kamar ’yan asalin jihar ba su san ta ba?

Alhamdu lillahi, duk da nan ba Arewa ba ce, su ma sun san muhimmancinta, suna saye suna kuma auna kwano-kwano. Wasu kuma suna zuwa su saya, kamar ta Naira 300 zuwa 50. 

’Yan asalin Jihar Kurosriba ne suka fi saye saboda suna nuna mana cewa sun san muhimmancinta kuma mata ma suna saye, masu sana’ar kunun aya.

Tsawon shekara 30 kana sana’ar sayar da aya, ko kwalliya ta biya kudin sabulu?

Alhamdu lillahi, kwarai kuwa, domin an yi aure, an yi suna, an yi gidaje duk da wannan sana’a. kannenmu ba mutum daya ba, ba biyu ba, sun je Saudiyya.

Ta bangaren ilmi fa, ko kuna tura yaranku neman ilmi na zamani?

kwarai kuwa, da ita dai wannan sana’a muke biyan kudin makarantar ’ya’yanmu, domin yanzu haka ma akwai wanda ya gama makaranta har aiki yake yi ana ma biyansa albashi kuma ta hanyar wannan sana’a aka dauki dawaniyar karatunsu yanzu.