Sana’ar Bola-jari: Muna taka sawun barawo — Shugaban ‘yan gwangwan

A kawo karshen wannan bala’i na bola-jari da yara kanana suka tsunduma.

Sana’ar Bola-jari: Muna taka sawun barawo — Shugaban ‘yan gwangwan

Shugaban Kungiyar Hausawa masu sana’ar gwangwan a Jihar Oyo, Alhaji Mukhtari Yakubu

Jari-bola sana’a ce da zamani ya kawo kuma matasa suka rungume ta sosai ganin yadda ake samun rufin asiri a cikinta.

Harkar tana cikin sana’o’in da mutum zai iya farawa ko ba shi da jari.

Ganin yadda masu sana’ar ke shiga juji da kazanta da hadari neman tarkacen karafuna da sauran abubuwa ya sa ake musu kallon kazamai da hadarin kamuwa da cututtuka ko samun raunuka.

Yadda suke bin dare da shiga lunguna da halayen wasunsu da kuma yadda barayi ke shigar burtu kamarsu kan sa a yi musu tambarin sata ko rashin gaskiya.

An sha smun mutane sun sana’ar. A wasu wuraren ana neman haramta sa’anar ko ma an haramta.

Akwai bukatar gwamnati  ta shigo harkar

Kabiru Tanimu mai shekara 45 a mai lura ne da yadda harkar jari-bola ke tafiya. Ya ce, “jari-bola na bukatar gwamnati ta shigo ta tsaftace harkar, ganin yadda babu wata hukuma da ke kula da ita.

Sayen kayan sata

“Matasa masu sana’ar jari-bola babu mai kula da harkokinsu, suna bata tarbiyyar yara da sayen kaya a hannun yara da suka tabbatar ba nasu ba ne.”

Shugaban kungiyar Hausawa ’yan bola-jari a Jihar Oyo, Alhaji Mukhtari Yakubu ya ce babbar matsalar da ’ya’yan kungiyar ke fuskanta ita ce yadda suke taka sawun barawo ake kama su haka kwai a wajen neman abincinsu.

Ya ce, “Akwai baragurbi da ba sa cikin kungiya da suka shiga sana’ar domin bata sunanmu.

“Tun daga lokacin da na zama shugaban kungiyar sai na dauki tsauraran matakai wajen hada kai da jami’an tsaro domin yaki da kuma dakile mugun nufin irin wadannan mutane.”

Bambancinta da gwangawan

Mutane kan dauka cewa jari-bola da sana’ar gwangwan daya ne, amma masu sana’ar gwangwan suna ganin yana da kyau a fayyacewa tsakaninsu.

Umar Muhammad wanda aka fi sani da Legas ya kwashe shekaru da dama yana sana’ar gwangwan a birnin Sakkwato, kuma ya bayyana wa Aminiya bambancin sana’ar da jari-bola.

“’Yan jari-bola su ne masu tsintar tarkace a kan hanya da kuma bola.

“Dan gwangwan kuwa shi ne mai saye da sayar da tsofaffin karafuna da karafunan da suka lalace da sauran tarkace.

“Jari-bola ba daya take da gwangwan ba, domin kuwa sana’ar gwangwan koyon ta ake yi don saye ne da sayarwa.

“Babban bambancin dan gwangwan da mai jaribola shi ne yadda kowanensu yake samo hajarsa.

“Duk wanda bai koyi sana’ar ba yana kwana ciki domin tana da ka’ida, sai ka zauna an koyar da kai domin kowace sana’a akwai rikita-rikita da kaddara.

“Duk inda zan sayi kaya sai na karbi rasit. Kalubalen da ke sana’ar gwangwan shi ne na sayen kayan sata.

“Wasu na iya hada baki a saci kaya su sayar maka, to nan ne za ka ga amfanin rasit da na zama dan kungiya.

“Dan gwangan karfen da yake saye mai kyau ne wanda mutane za su iya saya nan take su yi aiki da shi ko kuma kamfani ya yi amfani da shi.

“Amma dan bola tsinta yake yi a titi ko a bola. Idan ma sun sayi karfen mai kyau, to dan gwagwan suke kai wa.

“Kodayake duk harkar da mutum ke yi in bai tsabtace kansa ba yana kamuwa da cututtuka, amma dai masu sana’ar jaribola sun fi mu hadarin kamuwa da cuta,” a cewar Umar.

Amma Alhaji Mukhtari Yakubu ya shaida mana ofishinsa da ke sansanin ’yan gwangwan a unguwar Apata da ke Ibadan a Jihar Oyo cewa mahaifinsa ne ya koya masa sana’ar shekaru 30 da suka gabata.

“Ba haye na yi wa sana’ar gwangwan ba, gadar tan a yi. Kuma babu abun da zan ce sai godiya ga Allah da Ya azurta ni da dukkan abin da na mallaka a rayuwa.

“Na yi aure, ina da ‘ya’ya da jikoki na gina gida kuma na je Makka na sauke farali da sauran abubuwan rayuwa duka a cikin wannan sana’a,” in ji Alhaji Mukhtari.

Ya ce matakan da su dauka da mataimakansa domin tsaftace sana’ar gwangwan a Jihar Oyo sun yi tasiri wajen samun saukin yawan kamen da ake yi wa ’ya’yan kungiyar.

“’Ya’yan kungiyarmu a ko’ina suke za ka same su suna girmama doka da oda.

“Haka kuma muna yin aiki da shawarar jami’an kiwon lafiya da hukuma take turowa domin taimakawa wajen wayar da kanmu don kare kawunanmu daga kamuwa daga cututtukan da ke kunshe a cikin kayyakin kazanta da suke tabawa kodayaushe,” in ji shi.

Barazanar haramta sana’ar

Da yake tsokaci game da barazanar soke sana’ar gwangwan a wasu jihohin kasar nan, Alhaji Mukhtari Yakubu cewa ya yi, “babu irin wannan barazana a Jihar Oyo.

A maimakon haka ma gwamnati da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu sun bude wuraren da suke sayen kayan gwangwan daga hannunmu suna sake markada su zuwa kaya masu amfani.

“Ina yin kira ga gwamnatocin da ke yunkurin haramta sana’ar gwangwan su yi taka-tsan-tsan domin guje wa janyo wa kansu matsala.”

Shugaban ya yi tambaya cewa “Idan ka hana masu sana’ar gwangwan yin aiki a irin wannan lokaci na kuncin rayuwa to, wane tanadi ka yi masu?”

Rabi’u Muhammad wanda daya ne daga cikin shugabanni masu lura da sansanin ’yan gwangwan na Apata Ibadan, ya nemi mutanen da ke kallon sana’arsu a matsayin ta barayin zaune su daina bata sunan wannan sana’ar domin a cewarsa kowace sana’a tana tare da bata-gari.

Ya yi kira ga gwamnatocin jihohi su taimaka wajen bunkasa sana’ar jari-bola ta hanyar sanya ta cikin jerin sana’o’in da ake tallafa wa.

‘Tsadar rayuwa ta kawo mana cikas’

Shi kuwa Tanko Abdullahi mai tuka amalanken baro don nemo kayan bola-jari, cewa ya yi, “muna samun karancin irin kayan da muke tsinta a kan hanya saboda tsadar rayuwa ta sa wasu mutane suna rigerigen killace su domin sayar wa ’yan gwangwan.”

Akwai rufin asiri

Wani mai sana’ar a Gombe, Ibrahim Baban Bola, ya bayyana cewa wannan sana’a tana samar da rufin asiri, kuma ba kowace sana’a take samar da rufin asiri irin nata ba.

Ibrahim ya ce da sana’ar ya yi aure, yake ciyar da iyalinsa a yalwace tare da samun isasshen kudin da zai tafiyar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali.

A cewar sa, “muna sayen kilo na karfe a kan Naira 300, amma idan muka tara da yawa kuma muka kai kamfani, muna iya sayar da shi a kan Naira 500.

“Idan kuma ba ka son zuwa kamfani, sai ka sayar wa manyan ’yan kasuwa ka karbi kudinka, sannan ka sake tara wasu.”

Ya kara da cewa suna da yara da suke yawon nema musu karafan a kauyuka da sauran wurare, amma ba da kansu suke fita yawon nemowa ba.

Dokar hana sana’ar jari-bola

Bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da ta haifar da asarar kayayyakin jama’a da na gwamnati, an samu wasu da suke sayar da kayan da suka wawushe ga ’yan jari-bola.

Wannan ya sa gwamnatin Jihar Gombe ta kafa kwamitin da zai yi garambawul ga harkar, inda aka sanar da su cewa duk wanda aka samu yana sayar da kayan sata, zai fuskanci hukunci mai tsauri. Idan kuma hakan ya ci gaba, ana iya haramta sana’ar gaba daya.

Hadarin kamuwa da cututtuka

Wani jami’in lafiya mai suna Abubakar Nasir ya bayyana cewa kasancewar jari-bola sana’a ce da ake yin ta cikin kazanta kuma masu yin ta cikin hadarin kamuwa da cututtuka.

“Amma idan masu za su dingasanya safar hannu da wanke hannu kafin cin abinci tare da cin abinci mai gina jiki da kuma neman shawarar likitoci, za su yi ta su kare lafiya,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Idan kuwa ba su kiyaye ba, suna cikin hadarin kamuwa da cututtuka saboda kazantar da suke shiga wanda a hankali za ta iya jawo musu matsalolin lafiya.”

Bola-jari ba alheri ba ce

Sana’ar bola-jari ba alheri ne ba saboda yadda masu gudanar da wannan sana’ar ke rikidewa zuwa gudanar da sata ta hanyar fakewa da wannan bola-jari.

Masu lura da al’amurra da ke gudana a tsakanin al’umma suna nuni da illolin sana’ar bola-jari da matasa da kuma kananan yara ke yi da cewa babbar matsala ce ga cigaban al’umma.

A cewar wani jami’in tsaro da ke cikin al’umma, wanda ya nemi a sakaya sunansa, “dan gwangwan da barawo ba su da wani bambanci domin danjuma ne da danjummai.

“Shi dan gwangwan zaune yake yana jiran a kawo masa kaya ba tare da ya san yadda kayan suke ba kuma ya saya arha banza,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “’yan bola-jari suna shiga cikin gidajen mutane su kwashe musu tukwane da bokitai da kwanoni su dandake, su kai wa ’yan gwangwan.

“Haka nan kuma wadannan yara da ke zuwa nemo kayan gwangwan a karshe sukan kare ne da sace-sacen kayan mutane ta hanyar fakaitar idonsu.”

Ya ci gaba da cewa, “wani babban abin damuwar shi ne yadda yara ke kwana a garejin kanikawa suna balle karafa ko kuma su sace karafa da aka sayo domin gyara.”

A cewarsa, yanzu haka sun fito da wata hanya ta yadda suke yawo da buhu da kuma mayen-karfe suna jansa ta yadda suke janye karafa ba tare da mai shi ya gan su ba.

“Yanzu haka lamarin ya yi kamari inda ake zargin wasu daga cikin jami’an tsaro suna goya musu baya.

“Kusan duk wata satar kayan da ake na al’umma, kamar a makarantu da digar jirgin kasa da magudanan ruwa da sauran gurare, to ’yan bola ne, kuma suna hada kai da ma’aikatan da ke kulawa da su ne su sace su.

Ya ce, “Kai wani lokaci ma idan an kama irin wadannan bata-garin za ka ga jami’an tsaro da lauyoyi suna kaikomo don ganin cewa ba a hukunta su ba.

“Don haka suke zuwa wuraren da ake gine-gine suna fasa gini suna zare karafan rodi da aka yi amfani da su a ginin.”

Ya kara da cewa, “a halin yanzu dai lamarin jari-bola ya dauki sabon salo inda suke zuwa wuraren da ake aikin hanya suna yanke rodin da aka shimfida a gada ko a gefen hanya suna sayarwa ga ’yan gwangwan.”

Masanin ya bayyana cewa duk dabi’un ’yan bola-jari na tafiya ne kafada da kafada da ’yan gwangwan da ke daure musu gindi suna kwaso kayan jama’a suna kai musu.

Saboda haka ya shawarci hukumomin tsaro da kuma al’umma da su sanya ido tare da kawo karshen wannan bala’i na bola-jari da yara kanana suka tsunduma ciki musamman a wannan yanki na Arewacin Nijeriya.

 Tana hana zaman banza

Matasa na samun aikin yi da za su taimaki kansu har ma su taimaka wa iyayensu,”

Wani matashi da ke sana’ar a Jihar Katinsa mai suna Hassan ya ce tana hana zaman banza.

“Kamfanonin sarrafa robobi suke saye domin sake sarrafa su. Sannan akwai kwalaye da muke tsintowa a inda aka zubar mu sayar wa kafintoci ko kamfanonin da ke sake sarrafa su”.

Da yake amsa tambayar cewa a wasu lokutta ana aza zargin masu wannan sana’a suna fakewa da ita wajen daukar kayan mutane domin sayarwa ga masu kayan nauyi, sai ya ce. “E, ba za’a rasa bata gari ba, amma a ina wanda yake bin inda ake yin taro domin tsintar kwalba ko wanda ke bin bola inda ake zubar da shara don daukar matattar roba zai dauki kayan wani?

“Ba dai shiga gidaje muke yi ba, sai abin da muka ga an jefar.

“Sannan idan aka lura, za’a ga wannan sana’ar a yanzu tana hana matasan mu zaman banza, domin duk wanda ya ajiye girman kai, to zai samu alheri gare ta.”

Ya kara da cewa, “sannan sana’a ce mai bin ka’idar kasuwanci domin ana amfani da awon nauyi na sikeli.

“Matsalar dai kawai ita ce, cewa ba ka san abin da aka zuba can farko ga robar ko kwalin ba.

“Wannan ya sa muke fara wanke duk wata robar da aka kawo mana kafin mu sayar da masu sana’ar zuba wani abu a ciki ba.”