Sana’ar dogaro da kai ta fi tallafin N5,000 ga matasa – Suyudi

Honarabul Faruku Abdurrahamman Sayudi, shi ne Shugaban Majalisar Matasa ta Jihar Sakkwato shahararren dan siyasar gwagwarmaya ne a jihar. Aminiya ta zanta da shi kan al’amurran matasa da batun kudin da gwamnati tarayya ke son ta fara bayarwa gare su. Aminiya: Ko mai karatu zai iya sanin dalili ko makasudin da ya sanya ka shiga […]

Sana’ar dogaro da kai ta fi tallafin N5,000 ga matasa – Suyudi
Sana’ar dogaro da kai ta fi tallafin N5,000 ga matasa – Suyudi

Honarabul Faruku Abdurrahamman Sayudi, shi ne Shugaban Majalisar Matasa ta Jihar Sakkwato shahararren dan siyasar gwagwarmaya ne a jihar. Aminiya ta zanta da shi kan al’amurran matasa da batun kudin da gwamnati tarayya ke son ta fara bayarwa gare su.

Aminiya: Ko mai karatu zai iya sanin dalili ko makasudin da ya sanya ka shiga siyasa, har kake neman Shugabancin karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu?

Alhaji Faruku Abdurrahamman Sayudi: Siyasa dai hanyya ce ta rayuwa, ya zama dole kowane dan kasa nagari ya fito, ya ba da tashi gudunmuwa; kan wannan na sanya kaina cikin siyasa don ina da gudunmuwar da nake iya bayarwa a karamar hukumarmu da al’ummar Sakkwato gaba daya. Hakan ta sanya na fito na yi takara, in Allah ya ba ni jagorancin ina da tawa gudunmuwa, musamman ga matasa da harkokin gyaran gari da kuma sha’anin inganta tarbiyya da ilmi. Wadannan su ne kadan daga cikin dalilan da suka sanya na fito takara a jam’iyar APC.
Aminiya: Da yawa ‘yan siyasa sukan yi alkawurra kafin su dare saman kujera da zarar sun yi nasara. Abin ya sha bamban, to ko kai kana da wani tsari da zai bambantaka da sauran bara gurbin ‘yan siyasa?
Sayudi: Ina da shi gaskiya a lokacin da na fito takara tare nake tafiya da tsarin gudanar da gwamnatina a rubuce, kuma da shi nake yawo ana raba wa jama’a masu zabe su karanta, domin ya zama shaida tsakanina da su, in muka saba su jawo hankalina, har wasu sun kwaikwaye mu da aikata wannan, sai dai mu muna da tsari na tafiyar da al’amurra kan tsari, wanda ba za mu saba ba da yardar Allah. Kuma ba za mu yi siyasa ta kudi ba, don duk dan siyasar da ke amfani da kudi a siyasa ya mayar da ita sana’a ba hanyar rayuwa ba. Saboda in an ci zabe sai ya fara fitar da kudin sa da na iyayen gidansa da riba in akwai sauran lokaci, sannan a yi wa talakkawa aiki in babu shi ken an an tashi da su. Ba wai ina kore iyayen gida ne a siyasa ba, kowane dan siyasa yana da iyayen gida don su ne shugabannin jam’iyya, sai dai ya danganta daga tarbiyyar iyayen gidan za su dora shi kan hanyar kwarai ko muguwa. Wannan fafutika da muke yi, muna yinta ne don kishi da ci gaba, ganin yadda karamar hukumarmu take dada koma baya shekaru hudu da suka gabata, har zuwa yau in ka zagaya a mazabu 11 da muke da su ba za ka ga aikin Naira miliyan 10 ba. A matsayi na na dan karamar hukumar ban san shi ba, kuma ban gan shi ba in kana turaddadi ka tambayi al’umma ka ji. bangaren tarbiyya kuwa, ba wani katabus da aka yi, ilmi babu ci gaba, da wannan nike gaya maka za mu yi hobbasa mu da shugabaninmu na kowa gyara da canji mai alfanu don cika alkawarin da muka dauka da yardar Allah.
Aminiya: A matsayinka na Shugaban Majallisar Matasan Jihar Sakkwato, wanda ya dade yana gwagwarrmaya don kwato wa matasa hakkinsu, ya kake kallon dubu biyar da gwamnatin tarayya ta ce za ta bayar ‘yan majalisar dattiai suka tsayar da lamarin?
Sayudi: To ba bayar da kudin ne ke da muhimmanci ba, in an ba su tarbiyya da sana’ar yi ana iya bayar da tallafin ga gajiyayyu da marayu da marasa lafiya. Hakan zai taimaka, amma a wurin matasa sai dai a samo masu kyakkyawan ilmi da sana’o’in da za su aiwatar har su iya bai wa wasu wadannan kudin, ya fi a rike su nan ana ba su wannan tallafi don gudanar da rayuwa a nawa ra’ayi. Matasa a nemo musu sana’ar da za su dogara da ita. Dubu biyar a wata ba za ta rage rashin aikin yi ba, amma in aka bai wa gajiyayyu za ta yi matukar taimaka musu. In gwamnati ta yi la’akari akwai hanyoyi da dama da ake iya samar wa matasa harkar yi na dogaro da kai, wadanda za su yi rayuwa da su har su taimaki wani, ya fi a mayar da su almajirai
Aminiya: Wasu Matasa na korafi ba su da wakilci a Gwamnatin Buhari ko akwai abin da za ka gaya wa masu korafin?
Sayudi: Abin da ya kamata mutane su sani, matasa ko dattijai a harkar mulki, ba shi ne abin duba ba, mai kishi da son kasa da sanin ya kamata da dattako a ke dubawa. Cikin matasa da akasinsu, ci gaba muka sanya a gaba, ba jinsi ba. Kowa ya kamata ya ba da tasa gudunmuwa don a samar da ci gaba mai dorewa masu tasowa su amfana.
Aminiya: ’Yan adawa mabiya jam’iyar PDP a Jihar Sakkwato sun zargi Gwamnatin APC a jiha da kasa yin wani katabus a fiye da wata shida kuna kan karagar mulki?
Sayudi: Wannan ai soke-soke ne na siyasa, wanda kuma ba za ka hana dan siyasa ya fadi ra’ayinsa ba, amma in za su yi adalci ba a yin gaggawa wurin tsari don barnar da gwamnatin tarayya, wadda ta gabata ta yi shi ya dakatar da gwamnatocin jihohi, sai sun kimtsa ba wai gaggawa za su yi ba. Don ba za a iya gyara matsalar shekara 16 cikin wata shida ba, ba zai yiwu ba. Kan haka gwamnati na tafiya bisa tsari, ba za mu hana su yin suka ba, ko su yi mai ma’ana ko akasin hakan ba za mu hana su ba.
Aminiya: Ko kana da kira da za ka yi ga matasa?
Sayudi: Ina da shi, su sani duk wanda yake karami zai girma; matasanmu ya kamata su zama kyakkyawan misali don su ne manyan gobe. Mu ajiye maganar sare-sare da fadace-fadace da kuwa mu kalli shirye-shiryen da gwamnati ke kawo wa na cigabansu. A nan jihar gwamnati ta fito da shirye-shirye masu yawa, don bai wa matasa sana’ar yi. Irin wannan ya kamata matasa su sani dama ce, su bar wasa da ita, su bar sayar da kayan sana’ar da aka ba su ga wasu. Don ana tafiya da su a wasu jihohi a rika amfani da su a can. Allhamdulillah, an samu nasara kan kiraye-kirayen da aka rika yi ga matasa, wasu sun rike sana’a sosai. Muna son a yi koyi da wadannan don ganin lamarin gwamnati ya samu karbuwa.