Sana’ar fawa ta fi aikin albashi – Ladan Zaki

Wani mahauci a babban Kasuwar Waya da ke Bauchi Alhaji Ladan Zaki ya bayyana cewa a matsayinsa na wanda ya gaji sana’ar yana alfahari da fawa domin sana’ar ta masa riga da wando kuma yanzu haka yana da rufin asiri daidai bakin gwargwado. Ya ce: “Matuqar mutum zai riqe gaskiya da riqon amana, to fawa […]

Sana’ar fawa ta fi aikin albashi – Ladan Zaki

Alhaji Ladan ZakiWani mahauci a babban Kasuwar Waya da ke Bauchi Alhaji Ladan Zaki ya bayyana cewa a matsayinsa na wanda ya gaji sana’ar yana alfahari da fawa domin sana’ar ta masa riga da wando kuma yanzu haka yana da rufin asiri daidai bakin gwargwado.

Ya ce: “Matuqar mutum zai riqe gaskiya da riqon amana, to fawa da sauran tsoffin sana’oi da aka sani a tahirin qasar Hausa to tabbas cikin qanqanin lokaci Allah zai albarkaci abin da mutum yake samu.”
Har ila yau, ya ce ya kamata a fahimci cewa mahauta suna xaya daga cikin jerin mutanen da suke ba da gagarumin gudunmawa wajen bunqasa tattalin arzikin Najeriya. “Akwai masu sayar da naman tsire akwai masu balangu akwai kuma masu sayar da kilishi da dai sauransu. Dukkan jihohin qasar nan ko wace rana sai an yanka shanu da tumaki da akuyoyi masu ximbin yawa a kwata da sauran wuraren da hukumomi suka ware domin yanka,” inji shi.
Daga nan ya ce: “Watannin baya a Jihar Bauchi kowa yasan cewa ana sayar da Kilo xaya na naman saniya Naira 900 yanzu kuma ana sayarwa dubu 1350 sakamakon yadda abubuwa suka yi tsada a kasuwannin qasar nan. Jihar Bauchi tana xaya daga cikin jihohin da ake sayar da nama da tsire arha, amma ba kowa zai fahimci haka ba, sai wanda yake tafiye-tafiye daga arewa zuwa kudancin qasar nan.”
A qarshe ya shawarci ximbin matasa qasar nan da suka kammala karatu suna neman aikin gwamnati da su rungumi qananan sana’o’i.