Sana’ar fawa ta fi aikin gwamnati rufin asiri – Musa Katuka
Shugaban Cibiyar Sayar da Tsire ta (Katuka Special Meat) da ke kan titin kofaran a garin Bauchi Alhaji Musa Katukan ya bayyana cewa idan aka ci gaba da watsi da mahauta to tabbas nan da wani lokaci kadan za a fara fuskantar karancin naman sa a jihar domin sama da kashi 85 cikin 100 na […]
Shugaban Cibiyar Sayar da Tsire ta (Katuka Special Meat) da ke kan titin kofaran a garin Bauchi Alhaji Musa Katukan ya bayyana cewa idan aka ci gaba da watsi da mahauta to tabbas nan da wani lokaci kadan za a fara fuskantar karancin naman sa a jihar domin sama da kashi 85 cikin 100 na masu yanka suna fama da karancin dakunan sanyi na adana nama.
Sarkin Fawan Bauchi ya ce yana alfahari da sana’ar fawa domin tafi aikin gwamnati rufin asiri a wajensa. Ya ce duk wanda ya rike sana’ar fawa da gaske to tabbas zai samu rufin asiri bakin gwargwado.
Katuka ya kara da cewa sana’ar fawa tana daya daga cikin tsoffin sana’o’i a kasar Hausa, amma ya ce babbar matsalar da masu sana’ar suke fuskanta a jihohi daban-daban na kasar nan shi ne ba sa samu wani tallafi daga wajen gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi sakamakon haka dubban matasa sun jahilci ribar da ake samu ta albarkacin fawa.
Daga nan ya ce tun yana yaro yake aikin fawa kuma babu wata sana’a da na sani a rayuwa ta sai fawa saboda haka na bude wannan cibiya domin ganin na ba da tawa gudunmawar wajen dakile zaman kashe wando a tsakanin al’umma. Ya ce a yanzu akwai yara bakwai wadanda suke karkashina ina koya musu yadda ake aikin fawa da tsire.
“Dukkansu kowa yana samun abinda zai ci don haka ina kira da babbar murya ga matasan Najeriya don Allah a kama sana’a domin babu wata gwamnati a duniya da za ta bai wa kowa aikin yi dole wasu sai sun rungumi kananan sana’o’i,” inji shi.