Sana’ar fim ta koya mini alheri —Hadiza Gabon

Jaruma Hadiza Gabon ta ce farin cikinta shi ne ta ga ta kyautata wa mabukata.

Sana’ar fim ta koya mini alheri —Hadiza Gabon

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Aliyu, wacce aka fi sani da  Hadiza Gabon, ta ce harkar fim ta koya mata yin alheri da tausayin jama’a.

Hadiza Gabon, ta ce tsintar kanta a sanar’ar fim ta kara fahimtar da ita irin fikirorin da Allah Ya bai wa mata, wadanda ta ce sun taimaka mata matuka a rayuwa.

“Abun da ke sa ni farin ciki, ya kawar mini da damuwa, shi ne in ga na faranta wa gajiyayyu; Na fahimci cewa muna rayuwa ne da abin da muka dan samu, dan abin da muke ba wasu kuma da shi suke rayuwa.

“Yana da muhummanci mu fahimta cewa dan hobbasan da wani ya yi yana iya zama silar kyautatuwar rayuwar mutane da dama; sannan za a yi ta tuna hobbasan a matsayin aikin alheri.

“Ya kamata a kullum mu rika kokarin yin ababuwan da za su inganta rayuwar talakawa da gajiyayyun cikinmu.

“Masana’antar fim ta bude mini idanu a kan hakan, dalilin ke nan da ba na nadamar zama jarumar fim,” inji Hadiza Gabon.

Jarumar wadda da ta fara fitowa a 2009 a fim din Artabu, wanda da ya yi tashe sosai, ta ce tana farin ciki da sana’arta fim din da ta zabar wa kanta.

Ta ce tana matukar godiya ga Allah bisa nasarorin da ta samu a harkar fim da ma zaman ta jakadiya ga harkokin kasauwanci da dama a Najeriya.

Hadiza, wadda haifaffiyar birnin Libreville na kasar Gabon ce, mutum ce da aka yi wa shaida a matsayin mai sakin hannu da kuma saukin kai.

Bayanai sun nuna jarumar ta Kannywood ta jima da kafa gidauniyar tallafa wa gajiyayyu da kuma nuna musu kulawa.

“A 2016 na kafa gidauniyar Hadiza Aliyu Gabon (HAG), da zimmar kyautata rayuwar talakawa ta hanyar ba kula da ilimi da kiwon lafiyarsu da ma taimakon abinci daga dan abin da zan iya bayarwa,” inji ta.