Sanaár Gurguru: Ina cinikin Naira dubu 60 a kullum –Nafi’u Ibrahim
Malam Nafiú Ibrahim matashi ne da ya kafa wajen yin gurguru a wurare biyu a garin Kaduna. Ya kafa daya a bakin titin Dutsin-Ma da ke Tudun Wada Kaduna, yayin da ya bude na biyu a kusa da kasuwar Sheikh Abubakar Gumi a kusa da Mangal Plaza. Aminiya ta ziyarci inda yake gudanar da sanaár […]
Malam Nafiú Ibrahim matashi ne da ya kafa wajen yin gurguru a wurare biyu a garin Kaduna. Ya kafa daya a bakin titin Dutsin-Ma da ke Tudun Wada Kaduna, yayin da ya bude na biyu a kusa da kasuwar Sheikh Abubakar Gumi a kusa da Mangal Plaza. Aminiya ta ziyarci inda yake gudanar da sanaár yin gurgurun kuma ta tattauna da shi kamar haka:
Aminiya: Zan so na san cikakken sunanka?
Nafiú: Sunana Nafiú Ibrahim.
Aminiya: Shekarunka nawa?
Nafiú: Shekara ta 27.
Aminiya: Ina ne asalinka?
Nafiú: Ni Bahaushe ne kuma mutumin Kano.
Aminiya: Mece ce sanaárka?
Nafiú: Ina yin gurguru ne da injin yin gurguru irin na zamani.
Aminiya: Shekara nawa ke nan da ka fara wannan sanaá ta gurguru?
Nafiú: Yanzu ina cikin shekara ta uku kenan.
Aminiya: A ina ka fara koyon wannan sanaá?
Nafiú: Na fara koyonta ne a wajen wani maigidana a Kano, yayin da na samu ýanci ne na dawo Kaduna na bude nawa na kaina.
Na sanya wa sunan gurgurun da nake yi ‘dorayi Special Popcorn’ saboda daga unguwar dorayi da ke Kano na fito.
Aminiya: Idan mutum yana son ya bude wurin yin gurguru, nawa zai tanada a matsayin jari?
Nafiú: Mutum zai bukaci akalla Naira dubu 111. Wannan ya hada da sayen karamin injin da kuma kayayyakin hada gurgurun. Sannan ana bukatar injin bayar da wuta ga na’urar watau janerto, saboda matsalar dauke lantarki a kodayaushe.
Aminiya: To da me ake yin gurgurun?
Nafiú: Muna yi ne da masara da suga da zuma da mai da flabour da sauransu.
Aminiya: A ina kuke samun kayayyakin hada gurgurun?
Nafiú: Muna saye ne a nan garin Kaduna, musamman a kasuwar Kawo.
Aminiya: Ko ka samu izini daga Hukumar kula da ingancin abinci watau (NAFDAC) kafin ka bude wurin yin gurgurun?
Nafi’u: kwarai kuwa, ina da shaida. Don kafin na bude wannan wuri, sai da na yi rijista da su, saboda abu ne da ya shafi harkar abinci.
Aminiya: Cinikin nawa kake yi a kullum?
Nafi’u: Gaskiya nakan yi cikin akalla Naira dubu 60 a kullum don jama’a kan baibaye mu da zarar mun yi, suna saya, kamar yadda kake gani da idonka a halin yanzu.
Aminiya: Yanzu akalla yara nawa ke cin abinci a karkashinka?
Nafiú: Fiye da yara 50 na cin abinci a karkashina a kullum a wannan sana’a ta yin gurguru.
Aminiya: Nawa ne farashin da kuke sayar da kowace ledar gurguru?
Nafiú: Muna sayar da kowace leda a kan Naira 50, amma ga masu sari mukan ba su a kan Naira 40.
Aminiya: Wadanne garuruwa kuke kai gurgurun idan kun yi saboda sayarwa?
Nafi’u: A yanzu dai ban fara kaiwa nesa ba, saboda yanzu muke tasowa, amma ina da burin nan gaba na fara kaiwa wurare masu nisa. Mafi yawan jamaá kan same mu ne a inda muke yi suna saye, amma ga masu yin sari, ina tsammanin suna aikawa da shi wurare masu nisa, irin su Jihohin Neja da Kano da Katsina da Jigawa da sauransu.
Aminiya: Ta yaya kake biyan matasan da ke maka kasuwancin gurgurun? Ina nufin albashi kake ba su a duk wata ko a sati ko ya abin yake?
Nafiú: Muna biyansu ne ta hanyar kamasho, watau idan mutum ya sayar da ledar gurguru biyu yana da kason Naira 25 ka ga ke nan suna dawo mana da Naira 75 a duk gurguru biyu da suka sayar maimakon su ba mu Naira 100.
Aminiya: Wane kalubale kake fuskanta a wannan sanaá ta yin gurguru?
Nafiú: Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne a wasu lokuta masarar da muke amfani da ita takan baci da wuri, kuma hakan na janyo mana asara a mafi yawan lokuta, tun da ba kasafai ake gane masarar da ba ta da kyau ba, sai mun bude buhun muke ganewa. Sannan matsala ta biyu ita ce ta rashin isasshen jari. Sai kuma a lokacin damina ruwan sama kan hana masu yi mana talla su samu sukunin yin haka, tunda da ma a bakin titi suke tsayawa masu wucewa a abubuwan hawa suna saye.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu ?
Nafiú: Nasarar da na samu ba ta wuce ta yadda nake samar da sanaá ga matasa masu dimbin yawa a kullum ba. A kullum matasa kan yi tururuwa suna zuwa wajen da muke yin gurgurun ne don su rika yi mana talla a manyan titunan ababen hawa don samun na koko. Sannan yanzu haka na sake bude wani reshe na yin gurguru a Babbar Kasuwar Kaduna kusa da shagunan Mangal da ake wa lakabi da ‘Mangal Plaza’. Ka ga na mallaki waje biyu ke nan watau na nan da ke kan titin Dutsin-Ma da ke Tudun Wada Kaduna da kuma na kusa da Mangal Plaza a Kasuwar Sheikh Abubakar Gummi.
Aminiya: Mene ne burinka a wannan sanaá?
Nafiú: Babban burina shi ne in bude rassa a koína a fadin kasar nan.
Aminiya: Ka taba samun tallafi daga wajen wani ko gwamnati?
Nafiú: A gaskiya ban taba samun tallafin kowa ba, walau a daidaiku ko a gwamnatance, duk abin da ka gani a nan ni na saya da kudina.
Aminiya: Mene ne kiranka ga matasa?
Nafiú: Babban kirana ga matasa shi ne su tashi tsaye su nemi na kansu, kamar yadda Hausawa suke cewa sanaá saá.
Aminiya: Yaya batun iyali?
Nafiú: Ban yi aure ba, amma akwai niyya.
Aminiya: Batun karatun zamani fa?
Nafiú: A gaskiya ban yi karatun boko ba, amma na yi na Islama. Da ma tun farko aládarmu ita ce ta neman sanaár hannu, musamman ga mu Kanawa.
Aminiya: Mun gode!
Nafiú: Ni ma na gode, Allah Ya kara daukaka jaridar Aminiya, Allah Ya cigaba da taimaka wa maáikatanta a irin wayar da kan da kuke yi wa al’umma.