Sana’ar gyaran janareta ta yi min komai – Injiniya Shafi’u

Wani matashi kwararren mai gyaran janareta mai suna Injiniya Shafi’u Idris, ya bayyana sana’ar a matsayin sana’ar da ta  rufa masa asiri a rayuwa. Shafi’u wanda yake zaune ne a Jihar Gombe, ya ce ya kai kimanin shekaru bakwai yana yinta kuma har ya yaye yara kimanin guda bakwai wadanda suma yanzu suke cin gashin […]

Sana’ar gyaran janareta ta yi min komai – Injiniya Shafi’u
Sana’ar gyaran janareta ta yi min komai – Injiniya Shafi’u

Wani matashi kwararren mai gyaran janareta mai suna Injiniya Shafi’u Idris, ya bayyana sana’ar a matsayin sana’ar da ta  rufa masa asiri a rayuwa.
Shafi’u wanda yake zaune ne a Jihar Gombe, ya ce ya kai kimanin shekaru bakwai yana yinta kuma har ya yaye yara kimanin guda bakwai wadanda suma yanzu suke cin gashin kansu.
Ya ce babu wata sana’a da ya sani a rayuwa sai gyaran jannareta sai a lokacin da siyasa ta shigo ya sa kansa, inda yanzu haka shi ne shugaban matasa na jam’iyyar APC na unguwar Herwagana.
Ya kara da cewa kafin ya samu ya fara cin gashin kansa, ya taba zama karkashin maigidansa ne mai suna, Usman Abdullahi (Oga Manu) kana daga bisani aka yaye shi ya zama mai cin gashin  kansa.  
Da yake bayyana irin rufin asirin da yake tattare da sana’ar ya ce sana’ar ta rufa masa asiri ta hanyar daukar dawainiyar iyayensa sannan kuma da ita ya yi aure.  
Har ila yau, ya yi kira ga gwamnatin tarayya na ganin ta taimaka musu sun bunkasa sana’arsu.