Sana’ar kwado da linzami tana da rufin asiri -Abdullahi

Wani matashi da ke sana’ar kwado da linzami a Legas mai suna Abdullahi Babangida ya ce sana’ar ta fi wadansu sana’o’i rufin asiri. Malam Abdullahi Babangida mai shekara 36, wanda ya yi furucin haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya ya ce ya sami alheri sosai a sana’ar.Ya ce, “Babu shakka sana’ar kwado da linzami […]

Sana’ar kwado da linzami tana da rufin asiri -Abdullahi

Wani matashi da ke sana’ar kwado da linzami a Legas mai suna Abdullahi Babangida ya ce sana’ar ta fi wadansu sana’o’i rufin asiri. Malam Abdullahi Babangida mai shekara 36, wanda ya yi furucin haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya ya ce ya sami alheri sosai a sana’ar.
Ya ce, “Babu shakka sana’ar kwado da linzami ba abar rainawa ba ce domin, ni a ganina, ta fi sauran sana’o’i rufin asiri, domin ita za ka iya fitowa daga gidanka ba ka da ko sisi, amma da ka zo shago, sai ka koma gida da kudi aljihunka. Ka ga wadansu sana’o’in ba haka suke ba, dole sai ka tanadi kudi mai yawa kafin ka fara sana’ar ko kuma sai ka kashe kudi da yawa wajen sayen kayan aiki. Ita kuwa sana’ar kwado da linzami ba ka bukatar wasu makudan kudi wajen sayen kayan aiki”.
Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da na koyi sana’ar ina karami da yawa sun dauka harkar canji nake yi, wasu kuwa sun dauka aikin gwamnati nake yi, saboda kodayaushe suna ganina tsaf-tsaf ba alamun wahala a jikina. To ka ga idan ba rufin asiri, ta yaya za a rika yi maka kallon kana jin dadi?”
Ya bayyana cewa mahaifinsa Malam Babangida Tela shi ne ya sanya shi a sana’ar, yayin da wani mai suna Malam Abdullahi ya koya masa aiki, wanda kuma a lokacin bai fuskanci wani kalubale ba, saboda gatan da yake da shi a wurin mahaifinsa mai sana’ar tela, lamarin da ya jaza cikin wata uku ya koyi sana’ar, ba tare da wata wahala ba.
Malam Abdullahi ya kalla sana’ar kwado da linzami a matsayin sana’a ce ta gargajiya, wadda iyaye da kakanni suka bar wa ’ya’yansu da jikoki.
Wajen gudanar da ayyukan zayyanar kwado da linzamin, Malam Abdullahi ya yi nunin suna amfani da allura iri-iri, kamar babba da karama da zare kala-kala da robar da ake sanyawa a hannu da ake kira safi don maganin sukar allura. “Ina zayyanar fulawa a kwado da linzamin da aikin zube iri-iri. Nakan karbi misalin Naira dari biyar zuwa dubu daya har ma zuwa Naira dubu goma, a kan wannan aiki. Ya danganta da yanayinsa da kuma matsayin mai son sa. Babu abin da zan ce sai dai na gode wa Allah, Wanda ya taimaka mini har na yi aure a cikin wannan sana’a, lamarin da ya sa har muka haifi ’ya’ya biyar, wadanda duk da sana’ar nake ciyar da su da gudanar da sauran harkokin rayuwa”.
Malam Abdullahi ya ce yana da burin koya wa ’ya’yana wannan sana’a saboda na ga alfaninta. Ya rage ga abin da yaro yake so ya gudanar a can gaba, in ya girma, domin kowa da irin hanyar arzikinsa a rayuwa”. Inji shi.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50