Sana’ar sayar da keke ta yi min komai –Umar Mai Keke
Aminiya: Za mu so ka fara da gabatar da kanka?Sunana Umar Ahmad Abba, an haife ni a cikin garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a cikin Jihar Kaduna. A nan na yi karatun addini da na boko har zuwa lokacin da na fara harkar kasuwanci. Aminiya: A wane lokaci ka fara sayar da kekuna?Shekara shida da […]
Aminiya: Za mu so ka fara da gabatar da kanka?
Sunana Umar Ahmad Abba, an haife ni a cikin garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a cikin Jihar Kaduna. A nan na yi karatun addini da na boko har zuwa lokacin da na fara harkar kasuwanci.
Aminiya: A wane lokaci ka fara sayar da kekuna?
Shekara shida da suka wuce wato a shekarar 2010 na fara harkar sayar da kekuna. Abin da ya ja ra’ayina shi ne yadda na ga a wasu lokuta idan mutum yana bukatar zuwa wani waje don biyan wata bukata sai ka ga ba lallai ba ne ya samu abin hawa a irin lungun da yake, kuma a irin lokacin da yake bukata ba. Wani kuma dattijo ne da ake bukatar ya rika dan motsa jikinsa. Ga shi kuma sabbin kekuna sun yi tsada.
Abin da ya ja ra’ayina shi ne da farko ni ina zuwa Jihar Legas ne ina sayo kayayyakin da ke amfani da wuta da suka hada da talabijin da DbD zuwa firjin da sauransu. To a lokacin da na fara ganin kekunan sai ana dan ban sako in sayo guda uku, hudu, biyar haka ina dan samun wani abu ni ma.
Ana haka watarana na je sayen kayan wuta kamar yadda na saba, sai ya zama a daidai lokacin kuma dusar kankara ya mamaye wasu kasashea nahiyar Turai. Ta yadda ba za su iya turo da talabijin ba, ni kuma a daidai lokacin sai na ga tarin kekuna daga nan na fara tunanin an ya ba zan sayo su ba, haka dai na rufe ido da kudin da na je sayen kayan wuta kawai sai na sayo kekuna na kusan rabin miliyan.
Kawo kekunan da na yi na sauke a Kaduna, sai ya zama mutane na ta shigowa daga wurare daban-daban suna ta sayen kekunan nan abin har sai da ya ba ni mamaki, ta nan arewa ke nan. Su ko Inyamurai a can Legas wannan sayen kekuna da suka ga nayi sai su ma ya ja hankalinsu a kaina da zaran sun sauke kaya a can sai ya zama ni suke nema.
Ni kuma da na ga haka, sai nace bari in shiga da sunan Allah. Akwai wani a wancan lokacin ana ce masa Polo, shi ne farkon maigidana sai ya zama na ina aika masa da kudi shi kuma yana turo mini da kaya. To muna nan a haka har zuwa wani lokaci da aka cire tallafin mai (a lokacin Goodluck Jonathan), sai ya zama a daidai wannan lokacin shi maigidan nawa ya kawo kekuna, ga shi kuma kasuwansu ya dan yi kasa sosai shi ne a lokacin ya kira ni a kan in zo na ga kaya sun mishi yawa kuma shi yana so ya sayar ya koma. A lokacin da na je dubu dari uku ne kawai a tare da ni, amma haka ya ba ni kayan miliyan daya da dubu 20 cikin ikon Allah kwana biyu da shigowata da kayan Kaduna aka cire wannan tallafin. Sai ya zama a daidai lokacin mutanen Kaduna suka fara sanina kuma a nan Kaduna kawai, sai da na sayar da kayan wajen dubu dari bakwai da kyar na ware wasu na kawo su nan Kafanchan wanda suma a cikin daren aka zo aka saye su kudi hannu.
Har ila yau, a wancan lokacin akwai wani Inyamuri da yake sayar da mashina a Legas sunansa Tochukwu, amma saboda gaskiyarsa ana ce masa dan Izala. To shi wannan Inyamurin dan’uwansa ya tafi Japan sayo mashina, sai shi dan Izalan da ya ga yadda ake cinikin kekuna a lokacin sai ya kira dan uwan na sa ya ce ya turo masa kwantena daya na keke (wato kekuna dari shida ke nan). Bayan an turo masa sai ya rasa kwastoma duk wanda ya kira sai ya ki yarda sai aka ce masa akwai wani a Kafanchan ana ce masa Umar (wato ni), shi ne sai ya kira ni ya ce lallai ko jirgin sama zan shiga in zo Legas lallai-lallai in zo akwai kaya da aka sauke mishi in zo in gani. To ni kuma da jin haka sai na kira wani kwastomana a Kano ana ce masa Yunusa, na shaida masa ga wani kaya a Legas tirela daya ya ce in je in gani akwai wanda shi ma zai yi masa magana. Wallahi da na je na ga kekuna iya ganina a nan kasuwar unguwar Mile 12. Bayan na ga kaya sun yi kyau sai na kira Yunusan na shaida masa ya ce in zo da su kawai. Ina lodawa sai Kano, wannan shi ne karon farko da na kawo kwantena (wato tirela guda) nan arewa, kayan kusan miliyan uku da wani abu ke nan. Wallahi idan ka ga yadda Kanawan nan suka taru suna sha’awar irin kekunan sai ya baka mamaki domin ni ne na fara sauke rabin kwantena kuma ni na fara sauke kwantenan kekunan Belgium a arewa.
Tare da wannan Inyamurin da ake cewa dan Izala muka zo Kano, muka ba shi Naira miliyan daya ya koma. A halin yanzu duk Najeriya wannan Inyamurin shi ne babban dilan kekuna a Legas. Daga lokacin kawai sai harka ta bude mana aka fara nemana a Potiskum da Maiduguri da Bauchi da Gombe da kuma Kaduna a kan in kawo musu kaya. Akwai wani lokaci da na shiga Kano sai muka hadu da wani ana ce masa SBK yana sayar da kekuna da na yi masa magana sai ya ke ce mini, ai su ne suka fara zuwa da kekuna Kano na ce waye ogansa a Legas, sai ya ce mini dan Izala da na daga waya na kirasa sai ya shaida masa cewa ai sai da muka kwashe shekara uku muna harkar kafin ma SBK ya shigo harkar aka ce musu ai ni ne Umar Kafanchan. Nan suka cika da mamakin dama ni ne Umar, ai ni na kawo musu wannan arzikin! A yanzu ba wai fariya ba a sanadiyyar wannan harka ko mutum na tura Kano ko Biu ko Potiskum ko Gombe ko Bauchi ko Kaduna ko Zariya ko da bai san kowa ba, in na kira waya za a karbe shi hannu biyu, idan ma aure ne za su ba shi.
Akwai wani babban dan kasuwan kekunan da ya shahara a Legas an ace masa Rabi’u BB shi ma da yarona ne. Ni na hada shi da dan Izala.
Aminiya: Kafin harkar sayar da kekuna dama kayi wasu sana’o’i ne?
kwarai kuwa har abokaina na mini kirarin ‘Sana’a Goma’. Domin tun daga lokacin da na kammala aji uku na karamar sakandare na fara yi wa kaina tunanin kama wata sana’a da za ta rufa mini asiri. Kan haka, na fara da aikin Tinka, wato koyon gyaran tukwanen karfe da kwanuka a haka kuma idan damina ta zo aikin namu ya kan dan tsaya daga nan kuma sai in koma zuwa wani gari ana ce masa Matsirga ina saro rake in zo in yanka ina sayar.
Bayan nan nayi harkar sayar da yadudduka. Hakazalika, na yi aikin adashi, shi ma nan har ana kirana ‘Mai Adashin Maza da Mata’. Na sayar da takalma da kayan mata, na yi shagon sayar da littattafai (ni ma marubuci ne). Shagon waya da bidiyo club duka na yi su.
Aminiya: Menene bambancin kekunan Belgium ko kuma ‘Ladies’ kamar yadda kuke kira, da sababbin kekuna?
Gaskiya ba a hadawa domin tazarar na da yawa. Ka ga na farko in aka ce wannan abu sabo ne to duk ingancinsa za ka ga ‘yan Najeriya suna komawa wadannan kasashen da ke kera su, ana yi musu na su na daban wanda ake rage mishi karko da daraja. Za ka ga za a zo ana saidawa a zahiri, babu bambanci amma da an fara amfani da shi sai ka ga ya lalace nan da nan duk kyalkyalinsa kuwa.
Baya ga rashin amincin sababbin kekuna, akwai wahala wajen tukawa, sabanin Belgium wadanda suna da laushi ga canjin giya in kana son motsa jiki ga inda za ka danna in kuma sauri kake so ga giyan da zaka danna kuma ga gudu nan da nan zai kai ka duk inda kake so ka je sannan kuma ga su da wutan Sola, wato masu amfani da hasken rana da zaran dare ya yi za su kunna kansu sannan ga injin Sifili. Bambancinsu akwai yawa don saboda karkon Belgium ma har zaka gama morarta ka sayar ko ka kyautar tana nan da karfinta.
Aminiya: Ya batun kayan gyaransu, ana samu cikin sauki kamar na sauran kekuna?
Da farko an samu matsalar rashin samun kayayyakinsu kamar taya da tif. Hakan ya muka shiga damuwa don karamin abu in ya samesu sai dai a ajiye su. Ganin haka sai na koma wajen maigidana (dan Izala) na nuna masa gaskiya harkar nan za ta mutu in har ba a samun kayayyakin kekunan nan. To da ya kira dan uwan nasa ya shaida masa sai da aka yi tirela hudu na kayan gyaran kekunan Belgium, ka ji yadda muka yi muka samu mafita. Hakan ta sa Kanawa ma suka tafi China suka yo nasu odan, wasu suka tafi Japan daga nan dai komai ya yi kyau.
Aminiya: Ko za ka iya fada mana mutanen da ke ci a karkashinka?
Gaskiya da wadanda suka samu arziki da rufin asiri a sanadiyyata da kuma wadanda suke ci a karkashina suna da yawa. Ina da irin wadannan mutanen sama da 30 a Kano, haka a Kaduna da Zariya da Kafanchan.
Aminiya: Wadanne irin nasarori ka samu a wannan harkar?
Da farko dai na samu sanayya, kuma ka san an ce sabo da maza jari. Kyautatawa shi ne babban riba wanda a sanadiyyar haka mutane kan taso takanas daga wurare masu nisa musamman lokacin rasuwar mahaifina don su gaishe ni kawai. Cikin nasarorin na gina gida na kai mahaifiyata aikin hajji a shekarar 2013, da shekara ta kewayo (2014) na je na sauke farali. Bayan shekara guda wato a shekarar 2015 na kai matata ita ma aikin hajji duk a harkar sayar da kekuna sanna ga babban shagon keke da nake da shi a Kaduna ni kam na gode Allah.
Aminiya: Wadanne irin kalubale ka fuskanta?
daya daga ciki shi ne tashin Dala. Maimakon da, da zaka sauke mota sau uku a wata daya, yanzu sai dai ka sauke sau daya cikin wata uku. Matsala ta biyu ita ce bashi. Misali za ka ba mai gyaran keke kayayyaki ka ce ya dan gwada to idan ya gwada ya ji dadi in an zo maganar biya kuma sai ido ya raina fata.