Sana’ar sayar da zuma akwai riba- Malam Umaru
Wani fitaccen mai sana’ar sayar da zuma da amiya Malam Umaru Kwanar Dumawa ya ce sana’ar zuma tana da riba idan aka dubi irin alherin da masu yin ta suke samu musamman a wannan zamani.Malam Umaru ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan sana’ar sayar da zuma da kuma yin amiya, inda ya […]
Wani fitaccen mai sana’ar sayar da zuma da amiya Malam Umaru Kwanar Dumawa ya ce sana’ar zuma tana da riba idan aka dubi irin alherin da masu yin ta suke samu musamman a wannan zamani.
Malam Umaru ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan sana’ar sayar da zuma da kuma yin amiya, inda ya ce ya shafe fiye da shekara ashirin da biyar yana sana’ar sayar da zuma.
Ya ce ya samu rufin asiri dangane da wannan sana’a, sannan yana da abokan hulda masu yawa a sassa daban-daban na kasar nan har da Abuja da kudancin kasar nan.
Malam Mage ya ce da farko ya fara sana’ar sayar da itace, daga baya ya koma saka amiya yana sayarwa.
Ya bukaci masu sana’ar zuma su rika adalci, su guji yin algus, kasancewar yin hakan ba zai kai su ko’ina ba a rayuwa.