Sana’ar shayi sana’a ce mai daraja a duniya -Shugabanta na kasa

Shugaban kungiyar masu shayi ta kasa, Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana sana’ar shayi, sana’a ce mai daraja da mutunci a duniya. Alhaji Shu’aibu ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron mika shugabancin kungiyar, reshen Jihar Filato ga shugabannin riko da shugabannin kungiyar suka yi, bayan da wa’adinsu na shekaru hudu ya cika, a […]

Sana’ar shayi sana’a ce mai daraja a duniya -Shugabanta na kasa

Shugaba Alhaji Shu’aibu AbubakarShugaban kungiyar masu shayi ta kasa, Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana sana’ar shayi, sana’a ce mai daraja da mutunci a duniya.
Alhaji Shu’aibu ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron mika shugabancin kungiyar, reshen Jihar Filato ga shugabannin riko da shugabannin kungiyar suka yi, bayan da wa’adinsu na shekaru hudu ya cika, a ranar Asabar a Jos.
Ya ce masu sana’ar shayi su ke karbar baki a ko’ina a duniya, kuma shayi abu ne da kowa ya yarda shi a duniya, shi ya sa ma ya nemi gwamnatocin kasar nan su taimaka wa masu sana’ar ta kowace fuskar da ta dace don su habaka ta.
Haka nan ya yi  kiran gwamnatocin su kara daukar kyawawan matakan inganta kananan masana’antun kasar nan, domin samar da ayyukan yi ga matasa, “Saboda da yawa daga rikice-rikicen da ake samu a kasar nan, suna faruwa ne sakamakon rashin ayyukan yi ga matasa.
Shi ma a nasa jawabin, tsohon shugaban kungiyar na Jihar Filato da wa’adinsa ya cika, Alhaji Muhammad Abdullahi ya bayyana farin cikinsa kan irin goyon bayan da ’yan  kungiyar da jami’an tsaro suka ba shi, a tsawon shekaru hudu da ya yi yana rike da shugabancin kungiyar.
Ya bayyana cewa ya sami nasarori da dama a tsawon shekarun da ya yi a shugabancin kungiyar.
A nasa jawabin, wanda aka baiwa rikon shugabancin  kungiyar, Malam Nura Yusuf ya bayyana cewa za su yi iyakar kokarinsu wajen hada kan ’yan kungiyar tare da jawo su a jika da kuma inganta harkokin kasuwancin kungiyar a dukkan kananan hukumomin jihar 17.
Ya ba da tabbacin cewa da yardar Allah a  cikin watanni 3 da aka debar musu, za su gudanar da wadannan tsare-tsare tare da gudanar da ingantaccen zaben sababbin  shugabannin  kungiyar.  Don haka ya yi kira ga ’yan  kungiyar kan su ba da goyon baya da hadin kai, domin su sami damar aiwatar da ayyukan da aka dora musu.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50