Sana’ar shayin Ataye ta fi aikin ofis- Muntari
Malam Muntari Yusuf mai sayar da shayin Ataye ne a Jihar Katsina. Aminiya ta tattauna da shi inda ya bayyana rufin asirin da ya samu a sana’ar, har ma ta fi masa aikin ofis: Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanka?Muntari: Muntari Allah Wahid, an haife ni a garin Shantali ta gundumar Ajiwa a […]
Malam Muntari Yusuf mai sayar da shayin Ataye ne a Jihar Katsina. Aminiya ta tattauna da shi inda ya bayyana rufin asirin da ya samu a sana’ar, har ma ta fi masa aikin ofis:
Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanka?
Muntari: Muntari Allah Wahid, an haife ni a garin Shantali ta gundumar Ajiwa a karamar Hukumar batagarawa da ke Jihar Katsina a shekarar 1966. Ina sana’ar shayin Ataye.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka fara sana’ar shayin Ataye?
Muntari: Wani abokina ne mai suna Malam Surajo ya ba ni shawarar fara wannan sana’a. Ya ce sana’ar ba ta da wahala, kuma tana da saurin kawo riba. Na amince, sannan na tunkari wajen Mustafa da ke bakin Masallacin Juma’a don in koyi yadda ake yinta. Ka san in kana so ka mori kasuwanci to ka fara koyonsa ba wai kawai ka fada cikinsa ba. Da na fahimci yadda take, sai na fara da jarin da bai kai Naira dubu 20 ba, Allah Ya yi wa sana’ar albarka.
Aminiya: Yaya ita wannan sana’ar shayin Ataye take?
Muntari: To ita dai wannan sana’a ta sha bamban da ta masu sayar da shayin da ake zuba madara a hada da biredi. A da muna ganin Buzaye daga Nijar in sun zo wucewa da rakummansu, muna gani suna dafa shayi, to amma a wannan lokaci ba mu fahimci ashe magani ne ba. Sai mu yi ta gani sun dauki shan sa tamkar ibada, amma ba mu lura da irin yadda suke gudanar da harkokinsu cikin kuzari ba.
To a hankali mutanenmu suna shiga inda suke, kuma ana ba su suna sha har suka fara gane amfaninsa. Hade-haden ganyen itatuwa ne, wadanda mafi yawansu daga waje ake shigo da su. Ana kawo su daga kasar China, kasar da ta shahara a kan maganin gargajiya. Mukan samu wadannan ganyayyaki wadanda muke dafawa nan take mu bayar a sha. Akwai na maganin Basir da zazzabi da rage kiba da sauransu.
Aminiya: Yaya kake ganin wannan sana’ar?
Muntari: A gaskiya ni sanar sayar da shayin Ataye tafi aikin ofis a wajena. Ka ga wannan ganyen shayin sai in dora a murhu (Mangal), sannan in dafa shi, daga nan in zuba a kananan kofuna, amma gaskiyar magana abin da nake samu ya fi na mai aikin ofis, sai dai in yana kauce hanya. Ina biyan kudin haya kusan dubu 400 a shekara, sannan ina biyan gwamnati Naira dubu 50 a matsayin kudin haraji. Ga kudin makarantar yara da nake biya, ban da hidimomin yau da kullum.
Aminiya: Ko ka koya wa wadansu wannan sana’ar?
Muntari: Bayan koyarwa har yayewa nake yi, domin ko kwanan nan na yaye wasu, ga kuma wasu nan na koyo.
Aminiya: Me za ka ce a kan zargin da ake yi cewa masu wannan sana’ar na hada kayan maye?
Muntari: Farkon shigowa ta sana’ar na fuskanci wannan matsala ta masu shan kayan maye, wadda kuma ita ce babbar matsalar da nake fuskanta. Amma sakamakon bijire wa wannan dabi’ar sai hakan ya kara janyo mini manyan mutanen, kuma na gane akwai masu shigowa wannan sana’a da mummunar manufa, kuma na fadakar da ‘yan uwa don su tsaftace wannan sana’a, wadda hakan ya janyo har muka kafa kungiya. Ina tabbatar maka a yanzu idan har za a samu masu wannan dabi’a, to sai dai a boye.
Aminiya: To me za ka ce ga masu yi wa kananan sana’o’i kallon hadarin kaji?
Muntari: Ai ba karamar wauta suke yi ba, musamman ga matasa wadanda kullum zaman kashe wando ke kara yawaita a gare su. Ganin kana da ilmi ba hujja ba ce ka ce ba za ka yi sana’a ba. Kuma su irin wadannan kananan sana’o’i in ba a kula da su ba, to babu inda za a ci gaba. Mu dubi sauran kasashe hatta masu sana’ar wanke takalma suna da rawar da suke takawa wajen habaka tattalin arzikin kasa. Don haka na kira ga matasanmu da su rungumi sana’ar hannu komai kankantarta.