Sana’ar walda ta yi mini komai – Ashiru Tukur Maiwalda
Sana’ar walda wadda ta samo asali daga tsohuwar sana’ar kira. Aminiya ta gana da wani matashi mai suna Ashiru Tukur wanda yake sana’ar. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ko za mu ji takaitaccen tarihinka?Ashiru: Sunana Ashiru Tukur, an haife ni kimanin shekara 43 da suka wuce, a Unguwar Tudun Wada da ke nan cikin […]
Sana’ar walda wadda ta samo asali daga tsohuwar sana’ar kira. Aminiya ta gana da wani matashi mai suna Ashiru Tukur wanda yake sana’ar. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za mu ji takaitaccen tarihinka?
Ashiru: Sunana Ashiru Tukur, an haife ni kimanin shekara 43 da suka wuce, a Unguwar Tudun Wada da ke nan cikin Katsina. Na fara makarantar firamare a Kayalwa da ke cikin garin Katsina. Daga baya sai mahaifina ya gina gida a nan kofar kaura, inda na dawo nan makarantar kofar kaurar. Bayan na kammala na samu makarantar kwalejin horar da malamai harshen Larabci (ATC). Har ila yau, akwai wani makwabcinmu ana kiransa Abba Kasim. daya daga cikin kakannin masu waldar a nan a wancan lokaci Takubba suke yi,to ni kuma muna hira a kusa da kofar gidan in mun dawo kodai daga makarantar boko ko ta allo.
To ina ganin abubuwan da suke yi a hikimance har sai abin ya fara ba ni sha’awa. Abin yana burge ni a kan irin yadda na ga ana amfani da hikima har abin a hankali ya shiga raina sosai tunda ba ni da wajen hira sai nan kofar gidan. Daga nan ban san yadda aka yi ba har na tsinci kaina a cikin aikin ba.
Aminiya: Ko ka iya tuna abin da ka fara yi a ranar farko da ka fara aikin?
Ashiru: Kamar yadda na gaya maka, abu ne na yarinta wadda kawai sai na ganni ina aiki tare da su. Gaskiya ba zan iya tuna ranar ko abin da na fara yi ba. Sai dai abin da zance na fara yi na kwarai shi ne Tukwanen karfe. A lokacin na koyi tukunyar karfe. Allah cikin ikonsa, ina yin tukunya sai kuma aka koma wajen yin waldar. To sai na ga yin waldar ya fi ba ni sha’awa fiye da yin ita tukunyar karfen.
Aminiya: Kamar wadanne irin kaya ne mai walda yake bukata don gudanar da sana’arsa?
Ashiru: Ya tanadi injin da ake amfani da shi don yin waldar,sai wannan karfe da ake kira Bayis wanda ake budawa a rike karfe da shi, sai zarton yankan karfe, sai mabugi da sauransu.
Aminiya: Ko wannan sana’ar tana da wahalar koyo ne?
Ashiru: Ba zance ba ta da wahalar koyo ba, sai dai duk abin da Allah Ya nufe ka da yinsa, to zai yaye maka komai a kansa wanda zaka same shi babu wahala.
Aminiya: Ko akwai wadanda ka koya wa wannan sana’ar?
Ashiru: Eh, akwai su da dama.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta?
Ashiru: Abin da kowane lokaci nake tuna wa wanda kuma duk lokacin da na tuna sai na yiwa wannan mutun addu’a shi ne, wata rana ne ana son hada wayar gado,ya ce nine zan hada ta.
Kusan tun safe har zuwa Azahar ban hada wannan waya ba,kuma ya hana kowa ya nuna mani ko ya kama mani wallahi har sai da na yi kuka. Kuma ya ce, lallai sai na hada ta. Cikin ikon Allah zubar hawaye kawai sai Allah Ya ba ni ikon hada wayar gadon. Aka zo aka yi mini tabi saboda wannan kokari da na yi. Wallahi duk lokacin da na tuna wannan ba wai shi ba hatta da zuri’arsa ina yi masu addu’a.
Aminiya: Ko akwai wata fa’ida da ka samu albarkacin wannan sana’ar?
Ashiru: Alhamdulillahi, sana’ar walda ta yi mini komai a rayuwa. Gaskiya da za ace babu wani nauyi dake bisa kai irinsu biyan kudin makarantar yara da sauransu, a ce ana cikin walwalar komai, to ba wai ni ba A’a da ‘yan Najeriya sun ba duniya mamaki ta fuskoki da dama saboda Allah Ya ba mu kowace irin baiwa da ya bai wa mutum. Matsalarmu ita ce rashin wadatuwar wasu abubuwan. Ka tuna, yau za a kawo wani abu daga waje, amma idan Najeriya ya maimaita maka abin, sai ka kasa bambance su, kila ma na dan Najeriyar ya fi wancan.