Sana’ar wanke takalma ta fi yawon bara —yaro mai wankin takalma

Sana’ar wankin takalma sana’a ce da aka fi samun manyan mutane suna gudanarwa, amma wani yaro mai suna, Kabir Kabir da bai wuce shekara 10 ya fita daban da tsaransa, inda yake gudanar da ita. Aminiya ta yi kicibis da wannan yaro a cikin garin Katsina yayin da yake yawon neman mai bukatar aikinsa. Aminiya […]

Sana’ar wanke takalma ta fi yawon bara —yaro mai wankin takalma
Sana’ar wanke takalma ta fi yawon bara —yaro mai wankin takalma

Sana’ar wankin takalma sana’a ce da aka fi samun manyan mutane suna gudanarwa, amma wani yaro mai suna, Kabir Kabir da bai wuce shekara 10 ya fita daban da tsaransa, inda yake gudanar da ita. Aminiya ta yi kicibis da wannan yaro a cikin garin Katsina yayin da yake yawon neman mai bukatar aikinsa.

Aminiya : Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Kabir Kabir: Sunana Kabir Kabir domin sunan mahaifina aka sanya mani. An haife ni ne a unguwarmu Dutsin-Amare da ke nan Jihar Katsina, akalla shekaru 10 da suka wuce.
Aminiya: Mahaifanka na da rai?
Kabir Kabir: Eh. Kuma Bakaniken mota ne a kofar Marusa.
Aminiya: Kana zuwa makaranta?
Kabir Kabir: Ina zuwa. Ina zuwa makarantar Arabi da kuma boko. A yanzu aji na biyar a firamare.
Aminiya: Ku nawa ne a gidanku?
Kabir Kabir: Mu dai dakinmu mu shida ne.
Aminiya: Ga ka yaro, amma kuma kana sana’ar wankin takalma,yaya hakan ta faru?
Kabir Kabir: Da ita babanmu ke yi ni kuma sai na koya.
Aminiya: Babanka bai hana ka koyon ba ganin ka yi kankanta?
Kabir Kabir: A’a, bai hana ni ba.
Aminiya: Tun tsawon wane lokaci kake wannan sana’ar, kuma kana samun wani abu?
Kabir Kabir: Kusan shekara biyar ina yi kuma gaskiya ina samun ciniki.
Aminiya : Me ya ja hankalinka zuwa wannan sana’ar?
Kabir Kabir: Ina so in tashi da koyon sana’a tun ina yaro. Ya fi na je ina bara. Kuma kudin da na samu Innarmu nake ba har kuma ta sayo mini tunkiya. Kuma wani lokaci ina sayen wasu abubuwan da nake bukata ba sai na tsaya gida anyi mini ba.
Aminiya: Shin abokanka ba su yi maka dariya ko zaulaya?
Kabir Kabir: Suna yi mani, amma yanzu ba na bata rai kamar da farko saboda sana’a ce. Ko ma sun zo suna yi bani kula su.
Aminiya: Yaya kake samun sukunin zuwa makaranta?
Kabir Kabir: Ai sai an taso daga makarantar nike fita ko kuma ranar da ba’a makarantar.
Aminiya: Wadanne irin kayayyaki ne wannan sana’ar ke bukata?
Kabir Kabir: Akwai man da ake shafawa takalman bayan an wanke su da sabulu. Akwai gam da kusa da zare da kibiya ta dunke, inda ya cire da kuma wurin za ka zuba kayan.
Aminiya: Amma kamar ba waje guda kake tsayawa ba?
Kabir Kabir: Eh. Yawo nike yi, kuma ina samun ciniki. Na kuma saba bani jin komai a jikina.
Aminiya: Ko ka taba fuskantar wata matsala?
Kabir Kabir: A’a. Kawai dai wani lokaci in an kira ni na yi aiki sai a ga kamar bani iyawa. Sai kuma nayi aikin ,sai kuma a yi mamaki bayan farko da dariyar shegantaka za’a bani.
Aminiya: Wace shawara za ka ba yara kamarka da kuma matasan da suka kara ka?
Kabir Kabir: Sai dai na ce su je su koyi sana’a ya fi yawon bara ko maula. Idan suna sana’a za su iya yiwa kansu komai ba sai sun jira iyaye ko wasu sunyi maka ba, sai dai ma ka rika taimaka masu. Su kuma masu yi maka dariya indan har ba su kama sana’a ba, wata rana kai ne za ka yi masu.