Sana’ar wankin mota ta fi min komai —Matar aure

Hajiya Asama’u ta ce nan gaba za ta bude wurin wankin mota na mata zalla.

Sana’ar wankin mota ta fi min komai —Matar aure

Hajiya Asma’u Pate, matar aure ce da ke yin sana’ar wankin mota, wadda aka fi sanin maza da yi.

A tattaunawarta da Aminiya, ta ce ta fi son wankin mota fiye da duk wata sana’a da take yi ko ta taba yi saboda taimaka wa mutane da take yi a sana’ar.

Ta bayyana cewa nan gaba za ta bude wurin wankin mota wanda mata zalla ne za su rika gudanar da shi.

Ya aka yi kika fara sana’ar wankin mota?

To dama can ni ina da son kasuwanci a raina, domin ina iya tunawa nakan sayo kayan miya a unguwarmu sai in shiga makwabta in yi tallar sa da cewa na sayo ya yi mini yawa. Idan suka saya sai in dauki ribata in sake komawa in sayo wani.

To a haka na fara sayar da su zannuwan gado da tufafi da sauransu.

Amma ita sana’ar wankin mota na fara ta ne bayan da na je kasar Ingila wajen ’yar uwata.

Wata rana ina kallon wajen gidan sai na ga wata mace tana wankin motarta, sai abin ya birge ni.

Sai na gaya wa ’yar uwata cewa ina so idan na koma Najeriya na fara sana’ar wankin mota. Sai ta yi murmushi kawai.

Bayan kwana biyu sai muka sake yin maganar, da ta tattabatar da gaske nake yi, sai muka shiga kasuwa muka fara sayen kayan aikin.

Kafin na dawo Najeriya na tara kayayyakin wankin mota masu yawan gaske. Bayan na dawo sai na rika neman wurin da zan yi sana’ar.

To sai wata rana na zo wucewa ta wannan wurin sai na ga ana wankin mota a wurin da wani dan karamin inji.

Sai na je wurin na tambayi mutanen wanda ke da wurin. A lokacin ba ya nan don haka sai suka karbi lambar wayata cewa za su ba shi idan ya zo.

Sai kuwa ya kira ni a waya muka yi magana inda ya zo ya ga kayan da nake da su na aikin. Yana ganin irin kayyayakin da nake da su sai ya gamsu cewa da gaske nake yi.

Daga nan muka tsara yadda abubuwa za su kasance. Shi ke nan na fara wannan sana’a a shekarar 2011.

Lokacin da na fara haka za ki ga mutane sun kewaye wurin suna kallon mace na wankin mota, wasu har tambaya suke yi ko ni ba Bahaushiya ba ce da sauransu.

A lokacin da na fara sana’ar ni kadai nake gudanar da ita. Zan fito tun karfe tara na safe har zuwa karfe bakwai na dare.

Daga baya sai na dauki ma’aikata wadanda ke taimaka mini wajen gudanar da sana’ar.

Wadanne nasarori da kalubale kike fuskanta?

Na sami nasarori sosai domin mun bude wurin a sana’ar a rana mukan wanke sama da mota 40.

Koda yake sirrin nasarata ya dogara ne da yadda nake hulda da abokan cinikina.

Kalubalen sana’ar bai wuce irin matsalar da ake samu ta fuskar ma’aikata ba.

Kana tare da yaro ba ka san hawa ba balle sauka sai dai su shaida maka cewa zai yi tafiya da sauransu ko kuma ka tashi ma ba ka gan shi ba.

Akwai kuma wata matsalar ta ma’aikata da ba su yin aiki mai kyau sai a gabana.

A duk lokacin da na yi tafiya zan dawo na samu korafe-korafe masu yawa daga abokan huldata.

Wani kalubalen kuma shi ne yadda mutane ke kawo wankin kujeru ko kafet su bar mu da kaya a ajiye.

Wannan yana damu na domin za ki sami kujeru ko kafet da aka kawo wanki da ya shafe shekara biyu ba tare da an dauka ba.

Kuma abin da zai ba ka mamaki shi ne idan mai kayan ya zo, biya daya zai yi mana, babu ruwansa da wancan wankin da muka yi wa kayan, mu muka yi asarar jikinmu da kuma kayan aikinmu.

Ya za ki kwatanta sana’ar da sana’o’in da kike yi?

Idan kika duba sana’ar sayar da atamfofi ko zannuwan gado da nake yi, wanann ni kadai nake yin abina.

Amma wannan ina tare da mutane a karkashina.

A yanzu haka ina da yara 10 wadanda kuma kowanensu akwai tarin iyali a karkashinsa.

To wannan ne yake sa nake son sana’ar.

Alhamdu lillah, a yanzu haka ina tunanin bude wurin wankin mota na mata kadai wanda kuma nake so ya zama matan ne za su zama ma’aikata masu wankin motocin in sha’a Allah.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC