Sana’ar wankin takalmi ta canja rayuwata -Dahiru Shushaina
Wani mai sana’ar wankin takalmi da ke zaune a Legas mai suna dahiru Iliyasu ya ce sana’ar ta sauya rayuwarsa da ta iyalinsa.dahiru, mai kimanin shekara 30, dan asalin kauyen Liman-Ibada a Jihar Kaduna, ya yi furucin haka ne yayin wata tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata. “Babu shakka wannan sana’a ta […]
Wani mai sana’ar wankin takalmi da ke zaune a Legas mai suna dahiru Iliyasu ya ce sana’ar ta sauya rayuwarsa da ta iyalinsa.
dahiru, mai kimanin shekara 30, dan asalin kauyen Liman-Ibada a Jihar Kaduna, ya yi furucin haka ne yayin wata tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata. “Babu shakka wannan sana’a ta canja rayuwata, musamman kafin in koye ta, amma yanzu ina jin na zama mutum sosai. Ka ga a sana’ar nake ciyar da kaina da iyalina kuma har na taimaka wa ’yan uwa da abokan arziki. Ka ga babu rufin asirin da ya wuce wannan”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa sana’a tana da sirrinta da kuma rufin asiri, amma ba kowa ne ke gane haka ba. Su mutane sun dauka cewa sana’a bata lokaci ne, musamman idan suka dauke ta karama, sai su dauka kamar ba ya samun komai cikinta. “To ni na gode wa Allah da Ya sa har na koyi wannan sana’a kuma nake cin abinci a cikinta”.
dahiru, wanda ya shafe shekaru da dama yana sana’ar wankin takalmi, ya ce ya koye ta ne bayan ya samu matsala a kasuwancin sayar da takalma.
Ya kara da cewa a cikin haka ne yakan rika yin takalma iri-iri da suka hada da sau-ciki da sandal da mai igiya da marar igiya.
Ya ce yakan samu kimanin Naira dubu daya a kullum, kodayake yana da burin sauya wani abin da ya fi sana’ar wankin takalmi idan ya sami jari, amma a halin da ake ciki yana godiya ga Allah da yake samun abin rufin asiri na ciyar da kansa da iyalansa.
Ya ce a Arewa ana raina sana’arsu, “Amma nan kudu ana samun kudi da kayan aiki”.
Daga cikin kayayyakin aikin ya bayyana akwai kamar man goge takalmi da allurar dinki da ruwa da sabulu da fata da zaren lilo da kuma igiyar hada takalmi kala-kala.
A karshe ya shawarci matasa su daina yi wa sana’ar wankin takalmi kallon raini, domin sana’a ce da za ta rufa wa mutum asiri.