Sana’armu na cikin tsaka mai wuya —Masassaka turmi
Wasu masu sana’ar sassaka turmi da tabarya a Jihar Katsina sun roki gwamnati ta tallafa musu domin su ci gaba da aikin adana kayan amfanin da aka gada tun iyaye da kakanni. Sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa sun shafe shekaru masu yawa suna samun rufi asiri a sana’ar, don haka […]
Wasu masu sana’ar sassaka turmi da tabarya a Jihar Katsina sun roki gwamnati ta tallafa musu domin su ci gaba da aikin adana kayan amfanin da aka gada tun iyaye da kakanni.
Sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa sun shafe shekaru masu yawa suna samun rufi asiri a sana’ar, don haka suna bukatar tallafi da zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da kuma samar wa karin mutane ayyukan yi.
- Tsananin sanyi ya hallaka mutum 52 a Amurka
- Yadda ’yan bindiga suka kashe dogarin Shugaban Kamfanin Jirgin Kasa
“Babu wani tallafi da muke samu daga gwamnati, amma idan muka samu za mu inganta sana’armu; Idan gwamnati ta taimaka mana, za mu iya samun kayan aiki na zaman da za mu rika in sassaka da su,’’ in ji wani mai sana’ar a garin na Kankiya, mai suna Muhammad Sani.
Muhammad Sani ya bayyana a ranar Litinin cewa ya ce ya shafe shekaru yana sana’ar, kuma duk da sabbin fasahohin zamani, sana’ar tasu na bunkasa.
Ya ce mutane daga birane da manyan garuruwa kan sayi manya da matsakaitan turamen domin bukatunsu.
A cewarsa, bukatar turamen na karuwa ne saboda duk iyaye kan saya wa ’ya’yansu da za a yi wa aure.
Ya ce sukan sayar da kananan turame daga N3,000 zuwa N4,000; matsakaita kuma N10,000, manya kuma N17,000 ya danganci daga irin icen da aka sassaka.
Muhammadu ba bayyana cewa a kullum yana sassaka turame ya sayar wa dillalai, wadanda su kuma suke kaiwa kasuwanni.
Shi ma wani mai sana’ar, Muhammad Kafin-Dangi, ya tabbatar cewa ana sayen turame da tabaren da suke sassakawa a birane da kauyuka.
Shi ma ya roki gwamnati ta taimaka wa masu sana’ar domin bunkasa yanayinta da kuma samar da ayyuka.
(NAN)