Sanannen Kaduna
Wani Bakano ne ya zo Kaduna bakunta, sunansa Sabo. Da ya fita wajen kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, sai ya ji masu bas-bas suna cewa: “Sabo, Sabo, Sabo” (Suna nufin Unguwar Sabon Tasha). Shi kuma sai ya dauka shi ake kira. Da an ce “Sabo,” sai ya waiwaya yana daga hannu. Da ya koma gida […]
Wani Bakano ne ya zo Kaduna bakunta, sunansa Sabo. Da ya fita wajen kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, sai ya ji masu bas-bas suna cewa: “Sabo, Sabo, Sabo” (Suna nufin Unguwar Sabon Tasha). Shi kuma sai ya dauka shi ake kira. Da an ce “Sabo,” sai ya waiwaya yana daga hannu. Da ya koma gida sai ya rika cewa: “Ashe ni sananne ne a garin Kaduna, Domin da na je kasuwa, duk inda na waiga sai na ji ana cewa, Sabo, Sabo, Sabo!”
Daga Mudassir Ibrahim Mando